Lallai ni ina kan tafkina har in kalli wanda zai zo ya iso daga cikinku, za'a rike wasu mutane a kusa da ni, sai in ce: Ya Ubangiji daga gareni ne daga al'ummata ne

Lallai ni ina kan tafkina har in kalli wanda zai zo ya iso daga cikinku, za'a rike wasu mutane a kusa da ni, sai in ce: Ya Ubangiji daga gareni ne daga al'ummata ne

Daga Asma'u bint AbuBakar - Allah Ya yarda da su - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai ni ina kan tafkina har in kalli wanda zai zo ya iso daga cikinku, za'a rike wasu mutane a kusa da ni, sai in ce: Ya Ubangiji daga gareni ne daga al'ummata ne, sai a ce: Shin ka san abinda suka aikata a bayanka, wallahi ba su gushe ba suna komawa akan digadigensu".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa shi zai kasance a ranar Alkiyama akan tafkinsa dan ya ga wanda zai zo daga al'ummarsa zuwa tafkin, Kuma za'a rike wasu mutane a kusa da shi - aminci ya tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Ubangiji daga gareni ne kuma daga al'ummata ne, Sai a ce: Shin ka san abinda suka aikata bayan rabuwarka da su, wallahi ba su gushe ba suna komawa akan bayansu suna yin ridda daga addininsu, su ba sa tare da kai, kuma ba sa cikin al'ummarka.

فوائد الحديث

Rahamar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa da kuma kwadayinsa gare su .

Hadarin sabawa abinda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake akansa.

Kwadaitarwa akan riko da sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

التصنيفات

Imani da Ranar Lahira, Rayuwar Lahira, Rassan Imani