إعدادات العرض
Za'a kusantowa halitta da rana a yinin Alƙiyama har sai ta kusa kamar gwargwadan mil daga gare su
Za'a kusantowa halitta da rana a yinin Alƙiyama har sai ta kusa kamar gwargwadan mil daga gare su
Daga Miƙdad ɗan Aswad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «Za'a kusantowa halitta da rana a yinin Alƙiyama har sai ta kusa kamar gwargwadan mil daga gare su», Sulaim ɗan Amir ya ce: Na rantse da Allah ban san me yake nufi da mil ba? Shin faɗin ƙasa ne, ko kuma mil ɗin da ake wa ido kwalli da shi? - ya ce: «Sai mutane su zama akan gwargwadan ayyukansu cikin gumi, daga cikinsu akwai wanda zai kasance zuwa idanun sawunsa, daga cikinsu akwai wanda zai kasance zuwa guwoyinsa, daga cikinsu akwai wanda zai kasance zuwa kwankwasonsa, daga cikinsu akwai wanda zai yi masa linzmi linzami» ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi nuni da hannunsa zuwa bakinsa.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Tiếng Việt অসমীয়া Nederlands Kiswahili አማርኛ සිංහල ไทยالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa za'a kusanto wa halitta rana a yinin alƙiyama, har ta zama kamar mil ne daga kawunansu. Tabi'i Sulaim ɗan Amir ya ce: Na rantse da Allah ban san waɗanne mil ɗin ake nufi ba, shin faɗin ƙasa, ko kuma mil ɗin da akewa ido kwalli da shi? Ya ce: Sai su zama akan gwargwadan ayyukansu a gumi; daga cikinsu akwai wanda guminsa zai kai zuwa idanun sawunsa, daga cikinsu akwai wanda zai kai zuwa gwiwowinsa, daga cikinsu wanda zai kai zuwa kwankwasonsa da maɗaurin tazugensa, daga cikinsu akwai wanda guminsa zai kai zuwa bakinsa sai ya hana shi magana. Ya ce: Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi nuni da hannunsa zuwa bakinsa.فوائد الحديث
Bayanin tshin hankalin ranar alƙiyama da kuma tsoratarwa daga garesu.
Mutane zasu zama akan gwargwadan ayyukansu a cikin tsanani a ranar alƙiyama a farfajiyarta.
Kwaɗaitarwa akan ayyukan alheri, da kuma tsoratarwa daga ayyukan sharri.
التصنيفات
Rayuwar Lahira