Mune ƙarshen al'ummu, kuma waɗanda za'a fara yi wa hisabi

Mune ƙarshen al'ummu, kuma waɗanda za'a fara yi wa hisabi

Daga ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Mune ƙarshen al'ummu, kuma waɗanda za'a fara yi wa hisabi, za’a ce: Ina al'ummar nan ba'uwa da kuma Annabinta? mune na ƙarshe kuma na farko».

[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa al'ummarsa ita ce ƙarshen al'ummu a samuwa da kuma zamani, kuma ita ce farkon al'ummu da za’a yi wa hisabi a ranar alƙiyama, a ranar alƙiyama za'a ce: Ina al'ummar nan (ummiyya) ba'uwa da Annabinta? An dangantata ne zuwa ummiyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin rashin iya karatu da kuma rubutu. Za'a kirasu dan yin hisabi a farko, dan haka mune na ƙarshe a zamani da kuma samuwa, kuma na farko a hisabi da kuma shiga aljanna a ranar alƙiyama.

فوائد الحديث

Fifikon wannan al'ummar akan sauran al'ummu da suka gabata.

التصنيفات

Rayuwar Lahira