Wutarku wani yankine daga yanki saba'in daga wutar Jahannama

Wutarku wani yankine daga yanki saba'in daga wutar Jahannama

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wutarku wani yankine daga yanki saba'in daga wutar Jahannama", (Sai) aka ce: Ya Manzon Allah, ta kasance ta isa (dan azabtarwa), ya ce: "An fifita ta a kansu da yanki sittin da tara, kowannen su tamkar zafinta yake”.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wutar duniya wani yanki ne daga yanki saba'in daga wutar Jahannama, Wutar lahira karfin zafinta yana karuwa akan zafin wutar duniya da yanki sittin da tara, kowanne yanki daga gareta yana daidai da zafin wutar duniya. Sai aka ce : Ya Manzon Allah lallai cewa wutar duniya ta isa dan azabtar da masu shigarta. Sai ya ce: An fifita wutar Jahannama akan wutar duniya da yanki sittin da tara, kuma dukkaninsu tamkarta ne a cikin tsananin zafi.

فوائد الحديث

Gargadarwa daga wuta dan mutane su nisanci ayyukan da zasu kai su zuwa gareta.

Girman wutar Jahannama da azabarta, da kuma tsananin zafinta.

التصنيفات

Imani da Ranar Lahira, Sifar Al-janna da Wuta