إعدادات العرض
Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki
Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki
Daga Abu Sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki, sai mai kira ya yi kira: Yaku 'yan Aljanna, sai su dago kawunansu suna dubawa, sai ya ce: Shin kun san wannan? sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, dukkaninsu kuma sun ganta, sannan ya yi kira: Yaku 'yan wuta, sai su miko kawunansu suna dubawa, sai ya ce: Shin kun san wannan? sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu sun ganta, sai a yankata sannan ya ce: Ya ku 'yan Aljanna dawwama babu mutuwa, ya ku 'yan wuta dawwama babu mutuwa, sannan ya karanta: {Kuma ka yi musu gargadin ranar nadama yayin da aka hukunta al'amari alhali su suna cikin rafkana} [Maryam: 39], wadannan suna cikin rafkanannun mutane a duniya {Su ba su Imani ba} [Maryam: 39]".
الترجمة
العربية English မြန်မာ Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands اردو Español Bahasa Indonesia ئۇيغۇرچە বাংলা Türkçe Bosanski සිංහල हिन्दी Tiếng Việt മലയാളം తెలుగు Kiswahili ไทย پښتو অসমীয়া Shqip دری Ελληνικά Български Fulfulde Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy Română Kinyarwanda Српски тоҷикӣ O‘zbek नेपाली Moore Kurdî Oromoo Wolof Soomaali Français Azərbaycan Tagalog Українська தமிழ் bm Deutsch ქართული Português Македонски Magyar فارسی Русский 中文الشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa Za’a zo da mutuwa ranar Alkiyama, kamar siffar namijin tinkiya a jikinsa akwai fari da baki, Sai a yi kira: Ya ku 'yan Aljanna! sai su dago wuyan su da kawunansu suna dubawa. Sai ya ce da su: Shin kun san wannan?. Sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu hakika sun ganta sun kuma santa, Sannan mai kira ya yi kira: Ya ku 'yan wuta, sai su dago wuyansu su dago kawunansu suna dubawa. Sai ya ce: Shin kun san wannan?. Sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu hakika sun gan ta. Sai a yankata, sannan mai kira ya ce: Ya ku 'yan Aljanna wanzuwa har abada babu mutuwa,m. Ya ku 'yan wuta wanzuwa har abada babu mutuwa. Wannan dan ya zama kari a cikin ni'imar muminai, da masifa a cikin azabar kafirai. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta: {Kuma ka yi musu gargadi da ranar nadama a lokacin da aka hukunta al’amari alhalin kuwa suna a cikin rafkana, kuma ba su yin imani ba.} Ranar Alkiyama za'a rabe tsakanin 'yan Aljanna da 'yan wuta, kuma kowanne zai shiga inda zai dawwama a cikinsa. Sai mai munanawa ya yi nadama dan bai kyautata ba, mai takaitawa kuma dan bai kara alheri ba.فوائد الحديث
Makomar mutum a lahira ita ce dawwama a cikin Aljanna ko a wuta.
Gargadi mai tsanani daga tsoron Alkiyama kuma cewa ita ce ranar da na sani.
Bayanin dawwamar farin cikin 'yan Aljanna, da kuma dawwamar bakin cikin 'yan wuta.