Tafsirin Ayoyi

Tafsirin Ayoyi

5- Cewa wani mutum ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah ! ina da bayi biyu suna yi mini karya suna ha'intata suna saba mini, ni kuma ina zaginsu ina dukansu, ya matsayina yake garesu (a urin Allah?) Ya ce: "@Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, da kuma ukubar da ka yi musu*, idan ukubar da ka yi musu gwargwadan laifinsu ne, ya zama daidai wa daida, babu komai gareka ko akanka. Idan ukubar ka akansu kasa da laifin su ne to ya zama falala gareka, idan ukubarka garesu sama da laifin su ne za’a yi masu sakayyar karin daga gareka", ya ce: Sai mutumin yadan yi nesa sai ya fara kuka yana kururuwa, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin ba ka karanta littafin Allah ba: {zamu sanya ma'auni na adalci ga yinin Alkiyama ba za’a zalinci wata rai wani abu ba}. karanta zuwa karshenta, sai mutumin ya ce; Wallahi ya Manzon Allah, ban ji wani abu gareni dasu ba mafi alheri daga rabuwa da su, ina shaida maka cewa su 'ya'ya ne gaba dayansu.