Mabuɗan gaibu biyar ne

Mabuɗan gaibu biyar ne

Daga Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mabuɗan gaibu biyar ne, {Lalle, Allah a wurinSa kawai sanin yaushe Alkiyama zata tashi yake, kuma Yanã saukar da ruwan sama, kuma Yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai kuma wani rai bai san abin da yake aikatãwa a gõbe ba, kuma wani rai bai san a wace ƙasã yake mutuwa ba. Lalle Allah Masani ne Mai ƙididdidigẽwa}».

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Gaibu a wajen Allah babu wanda Ya san shi sai Shi, kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mabuɗan gaibu da kuma taskokinsa guda biyar ne: Na farko: Babu wanda ya san yaushe ne alƙiyama zata tsaya sai Allah, nuni ne zuwa ilimummukan lahira, domin ranar alƙiyama ne farkonta, idan sanin mafi kusa ya koru to sanin abin da ke bayansa ma ya koru. Na biyu: Babu wanda ya san yaushe ruwan sama zai zo sai Allah, nuni ne zuwa al'amuran duniyar sama, kuma an keɓanci ruwan sama ne tare da cewa yana da sabubban da suke nunin gudanar al'ada akan afkuwarsa sai dai cewa ba tare da tabbatarwa da kuma yaƙini ba. Na uku; Abin da yake kasancewa a cikin mahaifa; namiji ne ko mace, baƙi ne ko fari, mai cikakken halitta ne ko mai tauyayyar halitta ne, ɗan wuta ne ko ɗan aljanna ne da makamancinsu, kuma an keɓanci mahaifa da ambato dan mafi yawa suna saninta a al'ada, tare da hakan sai ya kore cewa wani ya zama ya san haƙiƙaninsu to waninsu ma shi yafi cancanta. Na huɗu: Babu wanda ya san abin da zai faru gobe sai Allah, nuni ne zuwa nau’ukan zamani da abin da ke cikinsu na abubuwan da zasu faru, kuma an yi amfani da lafazin: "Gobe" dan kasancewar haƙiƙarsa ta zama mafi kusancin zamaninnika, idan ya kasance tare da kusancinsa ba'a sanin abin da zai afku a cikinsa a haƙiƙa, tare da samun alama to abin da ya nisanta shi ne mamafi cancanta. Na biyar: Wata rai bata san a wacce ƙasa zata mutu, nuni ne zuwa wasu al'amuran duniyar ƙasa, tare da cewa al'adar mafi yawancin mutane ita ce ya rasu a garinsa sai dai hakan ba tabbas ba ne, kai da a ce ya rasu a cikin garinsa ba ya sanin a wani guri ne za'a binne shi a cikinsa, ko da ace akwai maƙabartar magabatansa, {Lallai Allah Masani ne Mai bada labari} Mai kewaye sani ne da zahiri da kuma baɗini, da abubuwan da ke ɓoye, da kuma sirrika, sai ayar ta haɗa nau'ikan gaibu, kuma ta gusar da ɓatattun da'awowi.

فوائد الحديث

Bayanin taskokin gaibu guda biyar waɗanda babu wanda ya sansu sai Allah.

Sindi ya ce: Faɗinsa: (Mabuɗan gaibu guda biyar ne), an ambaci waɗanda biyar ɗin: Mabuɗan gaibu; domin cewa duk wanda yake da waɗannan biyar ɗin to yana da bakiɗayan gaibu, sai suka zama kai kace dasu ne ake buɗe taskokin gaibu.

Ibnu Hajar ya ce: Ibnu Abi Jamra ya ce: Ya ambace su da mabuɗai dan kusanto da al'amarin ga mai ji; domin cewa duk abin da ya sanya shamaki tsakaninka da shi haƙiƙa ya ɓoye maka, kuma kaiwa zuwa ga saninsa a al'ada daga ƙofa ne, idan an kulle ƙofar sai a buƙatu zuwa mabuɗai, idan abin da ba'a tsinkaya akan gaibu sai an kai zuwa gare shi ba'a sanin bigirensa to ta yaya zai san abin da aka ɓoye.

Ibnu Abi jamra ya ce: Hikima cikin sanya su biyar nuni zuwa taƙaita nau'ikan halittu a cikinsu.

Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yakan bayyanar da wasu daga cikin gaibu ga manzanni, dan wata hikima daga gareShi.

Ɓata shacifaɗin masana taurari da bokaye a da'awarsu cewa sun san gaibu, kuma wanda ya yi da'awar wani abu daga abin da Allah - tarki ya tabbatar maSa - Ya kaɗaita da saninSa, to haƙiƙa ya ƙaryata Allah - Maɗaukakain sarki - da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma Alƙur'ani mai girma.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya, Tafsirin Ayoyi