إعدادات العرض
{Sannan lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima}
{Sannan lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima}
Daga Zubairu ɗan Awwam ya ce: Yayin da (aya) ta sauka {Sannan lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima} [Al-Takasur: 8], sai Zubair ya ce: Ya Manzon Allah, shin wace ni'ima ce za a tambayemu game da ita, bakake biyu ba ne kaɗai; dabino da ruwa? sai ya ce: "lallai dai kam daa sannu zai kasance".
[Hasan ne]
الترجمة
العربية English မြန်မာ Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands اردو Bahasa Indonesia ئۇيغۇرچە বাংলা Türkçe සිංහල हिन्दी Tiếng Việt తెలుగు Kiswahili ไทย پښتو অসমীয়া دری Кыргызча Lietuvių Kinyarwanda नेपाली മലയാളം Bosanski Italiano ಕನ್ನಡ Kurdî Oromoo Română Shqip Soomaali Српски Українська Wolof Tagalog Moore Malagasy தமிழ் Azərbaycan فارسی ქართულიالشرح
Lokacin da aya ta sauka: {Lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima} wato: Za a tambayeku game da tsayuwa da godiyar abin da Allah Ya yi muku ni'ima da shi, sai Zubair ɗan Al-Awwam - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah, shin wacce ni'ima ce za a tambayemu game da ita?! ni'imomi biyu ne kaɗai, da ba za su kai a tambaya ba, dabino ne da ruwa fa! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Lallai tabbas za a tambayeku game da ni'ima tare da wannan yanayin da kuke ciki, ni'imomi ne guda biyu masu girma daga ni'imomin Allah - Maɗaukakin sarki -.فوائد الحديث
Ƙarfafawa a kan godewa Allah - Maɗaukakin sarki - a kan ni'ima.
Ni'ima tana daga abin da za a yi tambaya game da ita a ranar Alƙiyama kaɗan ce ko mai yawa.