Lallai abin da kake faɗa kuma kake kira zuwa gareshi mai kyau ne, ina ma dai ka sanar da mu cewa akwai kaffara ga abin da muka aikata

Lallai abin da kake faɗa kuma kake kira zuwa gareshi mai kyau ne, ina ma dai ka sanar da mu cewa akwai kaffara ga abin da muka aikata

Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - Lallai wasu mutane daga mushrikai, sun kasance sun yi kisa sun yawaita, sun yi zina sun yawaita, sai suka zo wa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai suka ce: Lallai abin da kake faɗa kuma kake kira zuwa gareshi mai kyau ne, ina ma dai ka sanar da mu cewa akwai kaffara ga abin da muka aikata, sai (faɗin Allah) ya sauka: {Waɗanda ba sa kiran wani ubangiji tare da Allah, kuma ba sa kashe rai wanda Allah Ya haramta face da haƙƙi, kuma ba sa yin zina} [Al-Furqan: 68], kuma (wannan ayar) ta sauka: {Kace: (Allah Ya ce), "Ya ku bayiNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rayukanku! kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah} [Al-Zumar: 53].

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Wasu mutane daga mushrikai sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sun kasance haƙiƙa sun yawaita kisa da zina, sai suka cewa Annabi: Lallai abin da kake kira zuwa gareshi na musulunci da koyarwarsa abu ne mai kyau, sai dai halimmu da abin da muka afka a cikinsa na shirka da manyan zunubai, shin akwai kaffara a ciki? Sai ayoyi biyu suka sauka: Yayin da Allah Ya karɓi tuba daga mutane tare da yawan zunubansu da girmansu, da ba don haka ba, da sun zarce a kan kafircinsu da shisshiginsu da kuma ba su shiga wannan addinin ba.

فوائد الحديث

Falalar musulunci da girmansa kuma cewa shi yana rusa abin da ya gabata na zunubai.

Yalwar rahamar Allah ga bayinSa da gafararSa da rangwaminSa.

Haramcin shirka, da haramcin kashe rai ba tare da wani haƙƙi ba, da haramcin zina, da narko a kan wanda ya aikata waɗannan zunuban.

Tuba na gaskiya abin wanda ya hadu da ikhlasi da aiki na gari yana kankare dukkanin manyan zunubai har ma da kafircewa Allah - Maɗaukakin sarki -.

Haramcin yanke ƙauna daga rahamar Allah - tsarki ya tabbatar maSa -.

التصنيفات

Abubuwan da suke warware Musulunci, Tafsirin Ayoyi