Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su

Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su

Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Lallai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka, sai ya ce: "Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su, sabo da haka mutane sun kasu biyu: Mai biyayya ga Allah kuma mai tsoronSa mai girma a wajen Allah, da kuma fajiri taɓaɓɓe wulaƙantacce a wajen Allah, mutane 'ya'yan (Annabi) Adam ne, kuma Allah Ya halicci Annabi Adam daga turɓaya, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ya ku mutane lallai Mun halicce ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wurin Allah shi ne mafificinku a tsoron Allah, lallai Allah Masani ne kuma mai ba da labari [Al-Hujrat: 13].

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka sai ya ce: Ya ku mutane lallai cewa Allah haƙiƙa ya ɗauke kuma ya gusar muku da girman kan Jahiliyya, da jiji da kanta, da alfahari da iyaye, kawai dai mutane sun rabu gida biyu: Ko dai mumini mutumin kirki mai tsoron Allah mai biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, to, wannan mai girma ne a wajen Allah, ko da bai zama mai wani matsayi ko nasaba a wurin mutane ba. Ko kafiri fajiri taɓaɓɓe, to, wannan wulaƙantacce ne ƙasƙantacce a wurin Allah, kuma bai yi daidai da komai ba, ko da ya zama mai matsayi kuma yana da alfarma da mulki. Mutane dukkaninsu 'ya'yan Adam ne, kuma Allah Ya halicci Adam daga turɓaya, ba ya dacewa ga wanda asalinsa daga turɓaya ne ya yi girman kai ya yi jiji da kai, gasgata hakan shi ne faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Ya ku mutane lallai Mu Mun halicceku daga namiji da mace, kuma mun sanyaku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wajen Allah shi ne mafi tsoronku ga Allah, lallai Allah Masani ne Mai ba da labari} [Al-Hujurat: 13].

فوائد الحديث

Hani daga alfahari da dangantaka da kuma matsayi.

التصنيفات

Falalar musulunci da kyawawan koyarwarsa, Gamewar Musulunci g komai, Haqqin Xan Adam a Musulunci, Tafsirin Ayoyi