إعدادات العرض
Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi
Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce : «Lallai mafi ƙankantar matsayin ɗayanku a cikin aljanna shi ne Ya ce masa: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, sai Ya ce da shi: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce da shi: Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi».
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල Kurdî தமிழ் অসমীয়া Nederlands Kiswahili አማርኛ ไทยالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi ƙanƙantar matsayi da daraja ga wanda ya shiga aljanna shi ne Ya ce da shi: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, har sai ya zama babu wani burin da zai rage masa sai ya ambace shi , sai Ya ce masa: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce masa: To lallai kana da abinda ka yi burin dama kwatankwacinsa tare da shi.فوائد الحديث
Fifikon matsayin 'yan aljanna.
Bayanin girman karamcin Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
Ni'imar aljanna ba ta taƙaituwa akan wani ayyanannen abu, kai mumini zai samu dukkan abinda yake burinsa kuma ransa yake sha'awarsa dan falala da kyauta da kuma karamci daga Allah - Maɗaukakin sarki -.