إعدادات العرض
Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa, kofunansa sun fi yawan adadin taurarin sama
Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa, kofunansa sun fi yawan adadin taurarin sama
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah menene kofunan tafki? (Sai) ya ce: "Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa, kofunansa sun fi yawan adadin taurarin sama ku saurara a cikin duhun daren da babu hazo, kofunan Aljanna wanda ya sha daga garesu ba zai yi kishirwa ba har karshen al’amarinsa (na kishirwa), indararo biyu ne suke zuba a cikinsa daga Aljanna, wanda ya sha daga gareshi Ba zai yi kishirwa ba, fadinsa tamkar tsawonsa ne, tsakanin Amman zuwa Ailata, ruwansa ya fi nono tsananin fari, kuma ya fi zuma zaki".
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية English မြန်မာ Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands اردو Español Bahasa Indonesia ئۇيغۇرچە বাংলা Türkçe Bosanski සිංහල हिन्दी Tiếng Việt മലയാളം తెలుగు Kiswahili ไทย پښتو অসমীয়া Shqip دری Ελληνικά Български Fulfulde Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy or Română Kinyarwanda Српски тоҷикӣ O‘zbek नेपाली Moore Kurdî Oromoo Wolof Soomaali Français Azərbaycan Tagalog Українська தமிழ் bm ქართული Deutsch Português Македонски Magyar فارسی Русский 中文الشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa akan cewa kofunan tafkinsa a ranar Alkiyama sun fi yawan adadin taurarin sama, Wannan yana bayyana a cikin dare mai duhun da babu wata a cikinsa; domin kuwa dare mai wata taurari ba sa kasancewa a bayyane a cikinsa dan boyuwarsu da hasken wata, kuma wacce babu hazo a cikinta; domin samun hazo yana hana ganin taurari, Kuma cewa kofunan Aljanna, wanda ya sha daga abin shan dake cikin su ba zai yi kishirwa ba har abada, kuma wannan yana kasancewa karshen abinda yake samun mai shan na kishirwa. Kuma cewa tafkinsa indararo biyu daga Aljanna suna zuba a cikinsa, kuma fadinsa tamkar tsawonsa ne; Tafkin madaidaicin rukunai ne, tsawonsa yana kasancewa gwargwadan tazarar dake tsakanin Amman -ita wani gari ne a Balka'a daga Sham-, zuwa Ailata, wani birni ne sananne a gefen Sham. Ruwan tafkin ya fi nono fari, kuma dandanonsa ya fi zuma zaki.فوائد الحديث
Tabbatar da tafki da abinda ke cikinsa na nau'o'in ni'ima.
Girman tafkin da tsawonsa da fadinsa da yawan kofunan sa.
التصنيفات
Imani da Ranar Lahira