Farkon abinda za’a yi huknci a tsakanin mutane a ranar Alkiyama akan jini ne

Farkon abinda za’a yi huknci a tsakanin mutane a ranar Alkiyama akan jini ne

Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Farkon abinda za’a yi huknci a tsakanin mutane a ranar Alkiyama akan jini ne".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa farkon abinda za’a yi hukunci a tsakanin mutane a zalincin junansu a ranar Alkiyama: A jinane ne, kamar kisa da raunuka.

فوائد الحديث

Girman al'amarin jinane, domin farawa tana kasancewa ne da abu mafi muhimmanci.

Zunubai suna girmama ne da gwargwadan barnar da take afkuwa da su, salwantar da rayuka kubutattu yana daga mafi girman barna babu mafi girma daga gare shi sai kafirci da yi wa Allah - Madaukakin sarki - shirka.

التصنيفات

Rayuwar Lahira, Qisasi