Lallai cewa yana daga mafi sharrin mutane wadanda alkiyama zata riske su alhali suna raye, da wanda yake rikon kaburbura masallatai

Lallai cewa yana daga mafi sharrin mutane wadanda alkiyama zata riske su alhali suna raye, da wanda yake rikon kaburbura masallatai

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Lallai cewa yana daga mafi sharrin mutane wadanda alkiyama zata riske su alhali suna raye, da wanda yake rikon kaburbura masallatai".

[Hasan ne] [Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da mafi sharrin mutane, cewa sune wadanda alkiyama zata tsaya akansu alhali su suna raye, da wadanda suke daukar kaburbura masallatai, suna sallah a wurinsu suna kuma kallonsu..

فوائد الحديث

Haramcin gina masallatai akan kaburbura; domin hakan hanyace zuwa ga shirka.

Haramcin sallah a wurin kaburbura koda ba tare da gini ba; domin masallaci suna ne ga abinda ake sujjada a cikinsa koda babu gini a wurin.

Wanda ya riki kaburburan salihai masallatai dan yin sallah a wurin to shi yana daga mafi sharrin mutane, koda ya yi ikirarin cewa manufarsa neman kusanci zuwa ga Allah - Madaukakin sarki -.

التصنيفات

Alamomin tashin Al-qiyama