Shin kun san waye muflis (wanda aka yi wa wasoso)?

Shin kun san waye muflis (wanda aka yi wa wasoso)?

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin kun san waye muflis (wanda aka yi wa wasoso)? suka ce: Muflis a cikinmu wanda ba shi da dirhami ko kaya, sai ya ce: "Lallai cewa muflis daga al'ummata zai zo ranar alƙiyama da sallah da azumi da zakka, zai zo haƙiƙa ya zagi wannan, kuma ya yi wa wannan ƙazafi, ya ci dukiyar wannan, ya zubar da jinin wannan, ya daki wannan, sai a bawa wannan daga kyawawan ayyukansa, wannan ma daga kyawawan ayyukansa, idan kyawawan ayyukansa sun ƙare kafin a biya abin ke kansa sai a ɗauka daga kurakuransa sai a watsa masa, sannan a watsa shi a cikin wuta".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin kun san waye muflis? suka ce: Muflis a cikinmu wanda ba shi da dukiya ko kaya, sai ya ce: Lallai muflis daga al'ummata zai zo ranar lahira da ayyuka na gari na sallah da azumi da zakka. Kuma zai zo haƙiƙa ya zagi wannan, ya yi wa wannan ƙazafi a mutuncinsa, kuma ya ci dukiyar wannan ya yi musunta, kuma ya zubar da jinin wannan ya zalinci shi, ya daki wannan ya wulaƙantashi, sai a bawa wanda aka zalinta daga kyawawan ayyukansa, idan kyawawan ayyukan suka ƙare kafin ya biya abinda ke kansa na haƙƙoƙi da abubuwan da aka zalinta, sai a ɗauki zunuban wanda aka zalinta sai a sanya su a takardun azzalimin, sannan a watsa masa sai a jefa shi a cikin wuta inda babu wani kyakkyawan aiki da zai rage gare shi .

فوائد الحديث

Tsoratarwa ga afkawa a cikin abubuwan da aka haramta, musamman ma abinda ke rataye da haƙƙoƙin bayi na dukiya da na ma'ana.

Haƙƙoƙin mutane a tsakaninsu an gina su ne akan jayayya, haƙƙoƙin Mahalicci kuwa in banda shirka ababen ginawane akan afuwa.

Anfani da hanyar muhawara wacce zata sawa mai ji shauƙi kuma ta juyo da tunaninsa kuma ta motsa himmarsa, musamman ma dai a cikin tarbiyya da fadakarwa.

Bayanin ma'anar muflis na haƙiƙa, shi ne wanda waɗanda suke binsa bashi suka ɗauki ayyukansa na gari a ranar lahira.

Sakayya a lahira za ta iya zuwa a kan dukkanin kyawawan ayyuka, har sai ya zama ba zai rage wani abu ba daga cikinsu.

Mu'amalar Allah ga halitta mai tsayuwace akan adalci da gaskiya.

التصنيفات

Rayuwar Lahira, Munanan Halaye