Lallai wannan al'amarin zai kai inda dare da rana suka kai, kuma Allah ba Zai bar wani gidan bulo ko na gashi ba sai Allah Ya shigar da wannan addinin cikinsa

Lallai wannan al'amarin zai kai inda dare da rana suka kai, kuma Allah ba Zai bar wani gidan bulo ko na gashi ba sai Allah Ya shigar da wannan addinin cikinsa

Daga Tamimud Dari -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Lallai wannan al'amarin zai kai inda dare da rana suka kai, kuma Allah ba Zai bar wani gidan bulo ko na gashi ba sai Allah Ya shigar da wannan addinin cikinsa, da girman mai girma ko da ƙasƙancin kaskantacce, buwaya ce da Allah Yake ɗaukaka musulunci da ita, da ƙasƙancin da Allah Yake ƙasƙantar da kafirci da shi" Tamimi al-Dari ya kasance yana cewa: Haƙiƙa na san hakan a iyalan gidana, haƙiƙa wanda ya musulunta a cikinsu alheri da ɗaukaka da buwaya ya same shi, wanda yake kafiri a cikinsu kuma ƙasƙanci da wulaƙanci da jiziya sun same shi .

[Ingantacce ne] [Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wannan addinin zai game dukkan sasannin ƙasa, duk gurin da dare da rana suka kai gurin to wannan addinin sai ya kai wurin, Allah ba Zai bar wani gida a cikin birni ko alƙaryu ko a cikin ƙauyuka da sahara ba sai Ya shigar da wannan addini cikinsa. Wanda ya karɓi wannan addinin kuma ya yi imani da shi to zai zama mabuwayi da buwayar musulunci, wanda ya bijire masa kuma ya kafirce masa to zai zama ƙasƙantacce wulaƙantacce. Sannan sahabi Tamimud Dari - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya ga abinda manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata gare shi - ya bada labari da shi a iyalan gidansa musamman, domin wanda ya musulunta daga cikinsu alheri da ɗaukaka da buwaya sun same shi, wanda kuma ya kafirce daga cikinsu ƙasƙanci da wulaƙanci sun same shi tare da abinda zai dinga bayarwa na dukiya ga musulmai.

فوائد الحديث

Yi wa musulmi bushara cewa addininsu zai yaɗu a dukkan sasannin duniya.

Buwaya tana ga musulunci da musulmai, ƙasƙanci kuma yana ga kafirci da kafirai.

A ciknsa akwai dalili daga dalilan annabta da kuma alama daga almominta, yayin da al'amarin ya faru kamar yadda annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari.

التصنيفات

Alamomin tashin Al-qiyama