Allah Zai shigar da shi Aljanna akan aikin da yake akansa

Allah Zai shigar da shi Aljanna akan aikin da yake akansa

Daga Ubada - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, kuma Annabi Isa bawan Allah ne kuma ManzonSa ne kalmarSa ne da ya jefa ta ga nana Maryamu kuma Ruhi ne daga gare Shi, kuma aljanna gaskiya ce haka wuta ma gaskiya ce, Allah Zai shigar da shi Aljanna akan aikin da yake akansa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bamu labarin cewa wanda ya furta kalmar tauhidi yana masanin ma'anarta yana mai aiki da abinda ta hukunta, ya kuma shaida da ubudiyyar Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma manzancinsa, ya kuma yarda da kasantuwar Annabi Isa bawa ne na Allah da kuma manzancinsa, kuma cewa Allah Ya halicce shi da fadinSa "Ka sance" sai ya kasance , kuma cewa shi ruhi ne daga rayukan Allah wadanda Allah Ya haliccesu, ya kuma barrantar da babarsa daga abinda yahudawa suke jingina mata, ya yi imani da cewa aljanna gaskiya ce, kuma wuta gaskiya ce, yana mai kudirce samuwarsu, kuma cewa su ni'imar Allah ne da azabarSa, kuma ya mutu a kan hakan, to makomarsa tana aljanna koda ya kasance ya gajiya ne a ayyukan da'a, kuma yana da zunubai.

فوائد الحديث

Allah - Madaukakin sarki - Ya halicci Annabi Isa dan Maryam da kalmar (kasan ce) ba tare da uba ba.

Hadawa tsakanin kasancewar Annabi Isa da Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare su - bayin Allah ne kuma manzanninSa ne, su biyun Manzannin ne ba'a karyata su, kuma bayi ne (ga Allah) ba'a bauta musu.

Falalar tauhidi da kankarewarsa ga zunubai, kuma cewa makomar mai tauhidi ita ce aljanna koda wasu zunubai sun afka masa.

التصنيفات

Imani da Allah Maxaukaki, Imani da Ranar Lahira, Sifar Al-janna da Wuta