Lallai cewa ku zaku ga Ubanugijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba zaku wahala ba a ganinsa

Lallai cewa ku zaku ga Ubanugijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba zaku wahala ba a ganinsa

Daga Jariri dan Abadullahi - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Mun kasance a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya dubi wata a wani dare - yana nufin daren haske -(daran sha hudu ga wata) sai Ya ce: "Lallai cewa ku zaku ga Ubanugijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba zaku wahala ba a ganinsa, idan zaku iya kokarin kada a rinjayeku akan sallarku kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta to ku aikata" sannan ya karanta: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta}".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Sahabbai sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wani dare sai ya dubi wata - daren goma sha hudu -, sai ya ce: Lallai muminai za su ga Ubanbijinsu a hakika da ido ba tare da wani rikici ba, kuma cewa su ba za su yi cunkoso ba, kuma wahala ba zata samesu ba ko tsanani a yayin ganinsa - Madaukakin sarki -. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan kuna da ikon yanke abubuwan da zasu hana ku sallar Asuba da sallar La'asar to ku aikata, ku zo da su (Sallolin) a cike a lokacinsu a cikin jama'a, domin cewa hakan yana daga sabubban gani zuwa fuskar Allah - Mai girma da daukaka -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya karanta ayar: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kafin faduwarta}.

فوائد الحديث

Bushara ga masu imani da ganin Allah - Madaukakin sarki - a aljanna.

Daga hanyoyin Da'awa: Karfafawa da kwadaitarwa da buga misalai.

التصنيفات

Rayuwar Lahira