إعدادات العرض
Shin bana ba ku labari ba game da Jujal, wanda babu wani annabi da ya zantar da mutanensa shi ? lallai shi mai ido ɗaya ne, kuma shi zai zo a tare da shi akwai kwatankwacin aljanna da wuta,
Shin bana ba ku labari ba game da Jujal, wanda babu wani annabi da ya zantar da mutanensa shi ? lallai shi mai ido ɗaya ne, kuma shi zai zo a tare da shi akwai kwatankwacin aljanna da wuta,
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin bana ba ku labari ba game da Jujal, wanda babu wani annabi da ya zantar da mutanensa shi ? lallai shi mai ido ɗaya ne, kuma shi zai zo a tare da shi akwai kwatankwacin aljanna da wuta, wacce zai ce ita ce aljanna to ita ce wuta, lallai ni ina gargaɗarku kamar yadda (Annabi) Nuhu ya gargaɗi al'ummarsa da shi".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Kiswahili Português සිංහල دری অসমীয়া ไทย Tiếng Việt አማርኛ Svenska Yorùbá Кыргызча ગુજરાતી नेपाली Oromoo മലയാളം Română Nederlands Soomaali پښتو తెలుగు Kinyarwanda ಕನ್ನಡ Malagasy Српски Moore ქართულიالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ba wa sahabbansa labari game da Dajjal da siffofinsa da almominsa da abinda wani annabi a gabaninsa bai zantar da shi ba, daga hakan: Cewa shi mai ido ɗaya ne. Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanya masa kwatankwacin aljanna da wuta, gwargwdan ganin ido. Sai dai aljannarsa wuta ce, kuma wutarsa aljanna ce, wanda ya bi shi zai shigar da shi wannan aljannar a abinda mutane suke gani, sai dai cewa ita wuta ce mai ƙuna, wanda ya saɓa masa zai shigar da shi wutar a abinda mutane suke ganinsa, sai dai ita aljanna ce mai daɗi. Sannan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga fitinarsa kamar yadda (Annabi) Nuhu ya gargaɗar da mutanensa shi.فوائد الحديث
Girman fitinar Dujal.
Tsira daga fitinar Dajjal tana kasancewa ne da gaskiyar imani da fakewa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - da neman tsari da Allah daga gare shi a tahiyar ƙarshe, da haddace ayoyi goma daga farkon surar Kahfi.
Tsananin kwaɗayin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa, lokacin da ya bayyanawa musulmai siffofin Jujal abinda wani annabi kafin shi bai bayyana shi ba.