«‌Duk wanda ya zama yana da wani abin da ya zalinci ɗan uwansa da shi na mutuncinsa ne ko wani abu to ya yi ƙoƙarin warwarewa daga gare shi a yau, tun kafin lokacin da babu dinari ko dirhami*, idan yana da wani aiki na gari za'a ɗauka daga cikin shi gwargwadan zalincinsa, idan ba shi da wasu…

«‌Duk wanda ya zama yana da wani abin da ya zalinci ɗan uwansa da shi na mutuncinsa ne ko wani abu to ya yi ƙoƙarin warwarewa daga gare shi a yau, tun kafin lokacin da babu dinari ko dirhami*, idan yana da wani aiki na gari za'a ɗauka daga cikin shi gwargwadan zalincinsa, idan ba shi da wasu kyawawan ayyuka za'a ɗauka daga munanan ayyukan ɗan'uwansa (da ya zalinta) sai a jibga masa su».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Duk wanda ya zama yana da wani abin da ya zalinci ɗan uwansa da shi na mutuncinsa ne ko wani abu to ya yi ƙoƙarin warwarewa daga gare shi a yau, tun kafin lokacin da babu dinari ko dirhami, idan yana da wani aiki na gari za'a ɗauka daga cikin shi gwargwadan zalincinsa, idan ba shi da wasu kyawawan ayyuka za'a ɗauka daga munanan ayyukan ɗan'uwansa (da ya zalinta) sai a jibga masa su».

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci dukkan wanda ya aikata wani zalinci ga ɗan'uwansa musulmi a mutunci ne, ko dukiya, ko jini ya nemi wanda ya zalinta ya yafe masa tunda yana duniya, tun kafin ranar lahira ta zo, inda dinari ko dirhami ba za su yi amfani ba ga wanda ya baiwa wanda ya zalinta ba, dan ya fanshi kansa da shi ba; domin sakayya a wannan ranar da kyawawan ayyuka ne da kuma munana. Inda wanda aka zalinta zai kwasa daga kyawawan ayyukan azzalimin gwargwdan zalincinsa, idan azzalimin ba shi da wasu kyawawan ayyuka sai a labtawa azzalimin munanan ayyukan wanda aka zalinta gwargwadan zalincin da ya yi.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan nisantar zalinci da kuma ta'addanci.

Kwaɗaitarwa akan yin gaggawa dan kuɓutar da kawuna daga abinda suka rataya da shi na haƙƙoƙi.

Ayyuka na gari zalintar mutane da cutar da su yana ɓata su kuma yana tafiyar da amfaninsu.

Haƙƙoƙin bayi Allah ba Ya gafarta su, sai ta hanyar mai da su ga masu su.

Dinari da dirhami sune tsani na jawo abubuwan amfani a duniya, amma a ranar Lahira to sai dai kyawawan ayyuka da munana kawai.

Wasu daga cikin malamai sun faɗa a cikin mas'alar Irbad: Idan wanda aka zalinta bai sani ba to babu buƙatuwar ya sanar masa, misali a ce ya zage shi a wani wuri daga cikin wurare kuma ya tuba, to a nan shi babu wata buƙatuwa ya sanar da shi, saidai babu bukatar ya sanar da shi , saidai ya nema masa gafara, kuma ya yi masa addu'a, ya yabi alherinsa a wuraran da ya zage shi a cikinsu, da haka ne zai warware daga gare shi .

التصنيفات

Rayuwar Lahira