إعدادات العرض
Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar
Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar
Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Muna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci sai wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya dirkusar da shi a cikin masallaci sannan ya daure shi, sannan ya ce da su: Waye Muhammad a cikinku? alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide a tsakaninsu, sai muka ce : Wannan farin mutumin wanda ke kishingide. Sai mutumin ya ce da shi: Ya kai Dan Abdul Mudallib sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: "Hakika na amsa maka". Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji haushi na a ranka? sai ya ce: "Ka tambayi abinda ya bayyana gareka" sai ya ce: Ina tambayarka dan Ubangijinka da Ubangijin wadanda suka gabaceka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane gaba dayansu? sai ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu yi salloli biayr a yini da dare? ya ce: "Eh ya Allah ne.” ya ce Ina maka magiya da Allah shin Allah ne Ya umarceka da mu yi azumin wannan watan a shekara? ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce; Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawan mu? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Eh ya Allah". sai mutumin ya ce; na yi imani da abinda ka zo da shi, kuma ni manzo ne na wadanda ke bayana cikin mutane na, Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar.
الترجمة
العربية English မြန်မာ Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands اردو Español Bahasa Indonesia ئۇيغۇرچە বাংলা Türkçe Bosanski සිංහල हिन्दी Tiếng Việt മലയാളം తెలుగు Kiswahili ไทย پښتو অসমীয়া Shqip دری Ελληνικά Български Fulfulde Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy Română Kinyarwanda Српски тоҷикӣ O‘zbek नेपाली Moore Kurdî Wolof Soomaali Français Oromoo Azərbaycan Tagalog Українськаالشرح
Anas dan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa: Lokacin da sahabbai suna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci yayin da wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya durkusar da rakumin sannan ya daure shi. Sannan ya tambayesu: Waye Muhammd a cikinku? Alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide tsakanin mutanen, sai muka ce : Wannan farin mutumin. Sai mutumin ya ce da shi: Yakai Dan Abdul Muddalib. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: Na ji ka yi tambaya in amsa maka. Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne kuma mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji wani abu game dani a ranka. Wato: Kada ka yi fushi da ni kuma kada kunci ya sameka. Sai ya ce: Ka tambayi abinda kake so. Sai ya ce: Ina ina hada ka da Ubangijinka kuma Ubangijin wadanda suka gabace ka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane? Sai ya ce: Eh ya Allah, dan karfafa gaskiyarsa. Sai Mutumin ya ce: Ina yi maka magiya da Allah, wato; Ina tambayarka sabo da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka yi salloli biyar a yini da dare? Su ne salloli wadanda aka faralanta ?., Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu azimci wannan watan daga shekara? wato: Watan Ramadan, Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka daka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawanmu? ita ce zakka. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Eh ya Allah, Sai Dimam ya musulunta, kuma ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa shi zai kira mutanensa zuwa Musulunci. Sannan ya yi bayanin kansa cewa shi ne Dimam dan Sa'alabata daga Banu Sa'ad Ibnu Bakar.فوائد الحديث
Tawali'un Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -; dan mutum ba zai iya banbancewa ya raba tsakaninsa da sahabbansa ba.
Kyakkyawar dabi'un Annabi - aminci ya tabbata agare shi -, da tausasawarsa a bada amsa ga mai tambaya, kuma cewa kyakkyawar bada amsa tana daga sabubban karbar Da’awah.
Halaccin bayanin mutum da wata siffa na fari da ja, da tsawo da gajarta, da makamancin wannan daga abinda ba'a nufin aibatawa da shi, idan ba ya kin hakan.
Halaccin shigar kafiri masallaci dan bukata.
Bai ambaci Hjji ba a cikin hadisin domin cewa shi zai iya kasancewa ba'a wajabta Hajjin ba a lokacin zuwansa ba.
Kwadayin sahabbai akan kiran mutane; daga musuluntarsa ya yi kwadayin kiran mutanensa.