Kada a bar wuyan wani raƙumi da wani abin wuya na tsirkiya, ko wani abin wuya dai sai an yanke shi

Kada a bar wuyan wani raƙumi da wani abin wuya na tsirkiya, ko wani abin wuya dai sai an yanke shi

Daga Abu Bashir mutumin Madina, Allah Ya yarda da shi: Cewa ya kasance tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a wasu tafiye- tafiyansa, ya ce: Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aika a lokacin munane suna wurin baccinsu Kada a bar wuyan wani raƙumi da wani abin wuya na tsirkiya, ko wani abin wuya dai sai an yanke shi.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance a wata tafiyarsa a lokacin mutane suna wurin baccin su inda suke bacci a bukkokinsu da shemominsu. Sai ya aika wani mutum don ya sami mutane ya umarcesu da yanke kowanne abu da aka rataya a wuyan raƙumi, shin na tsirkiya ne, ko wani abu kamar ƙararrawa ko takalmi, domin sun kasance suna yi musu rataye saboda tsoron kambun baka, sai aka umarce su da su yanke, domin babu abin da take karawa, kuma anfanarwa da cutarwa suna hannun Allah ne Shi kadai.

فوائد الحديث

Haramcin rataya tsirkiya da abin wuya domin janyo amfani ko kuma tunkuɗe cuta domin haka nau'i ne na shirka.

Sanya abin wuya wanda ba tsarkiya ba, idan ya kasance domin ado ne ko jan dabba ko ɗaureta, to, wannan babu komai.

Wajibcin hana ɓarna gwargwadon iko

Wajibcin ɗamfaruwar zuciya da Allah shi kaɗai babu abokin tarayya da shi.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya