إعدادات العرض
Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta azaba a ranar lahira: Shin da ace duk abinda ke cikin ƙasa naka ne shin zaka fanshi kanka da shi? Sai ya ce: Eh
Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta azaba a ranar lahira: Shin da ace duk abinda ke cikin ƙasa naka ne shin zaka fanshi kanka da shi? Sai ya ce: Eh
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta azaba a ranar lahira: Shin da ace duk abinda ke cikin ƙasa naka ne shin zaka fanshi kanka da shi? Sai ya ce: Eh, Sai ya ce: Na so ƙasa da hakan daga gareka alhali kai kana cikin tsatson (annabi) Adam: Kada ka ka yi min tarayya da wani abu, sai kaƙi sai dai ka yi shirka daNi".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt Kurdî Português සිංහල অসমীয়া Kiswahili አማርኛ ગુજરાતી Nederlands پښتو नेपाली ไทย മലയാളം Кыргызча Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta a zaba bayan shigarta: Da ace duniya da abinda ke cikinta nakane shin zaka fanshi kanka da ita daga wannan azabar? Sai ya ce: Eh, Sai Allah Ya ce: Haƙiƙa Na nema daga gareka kuma Na umarceka da mafi sauƙi daga hakan lokacin da aka karɓi alƙawari gareka alhali kai kana cikin tsatson (annabi) Adam da kada ka yi shirka daNi da wani abu; sai kaƙi lokacin da Na fitar da kai zuwa duniya sai dai shirka.فوائد الحديث
Falalar Tauhidi da sauƙin aiki da shi.
Haɗarin shirka da Allah - Maɗaukakin sarki - da ƙarshenta.
Allah Ya riƙi alƙawari ga 'ya'yan Adam a bayan babansu Adam da rashin yin shirka.
GargaɗI akan shirka kuma cewa duniya gabaɗayanta ba zata wadatar da kafiri da komai ba a ranar lahira.
التصنيفات
Tauhidin Uluhiyya