Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi ba, ya aibanta Ni kuma hakan bai kamata ya faru daga gare shi ba

Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi ba, ya aibanta Ni kuma hakan bai kamata ya faru daga gare shi ba

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Madaukakin sarki ya ce: ‘Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi ba, ya aibanta Ni kuma hakan bai kamata ya faru daga gare shi ba. Amma karyatawar shi gare Ni shi ne fadinsa: (Allah) ba zai dawo dani ba (bayan mutuwa) kamar yadda Ya halicce ni a farko, ba wai halittar ta farkon ita ce mafi sauki gareNi daga dawowa da shi ba, amma aibantaNi shi ne fadinsa a kaina: Allah Yana da Da, alhali Ni Daya ne kwal wanda ake nufinSa da bukata Ban haifa ba, ba’a kuma haifeNi ba, kuma babu daya da ya kasance tamka a gare Ni".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyanawa acikin Hadisi Kudsi cewa Allah - Mai girma da daukaka - Ya sanar game da mushrikai da kafirai cewa su suna karyataShi suna siffantaShi da tawaya da aibobi, kuma hakan bai kamacesu ba. Amma karyatawar da suka yi wa Allah: Ita ce riyawarsu cewa Allah Ba zai dawo da su bayan mutuwarsu ba akaro na gaba, kamar yadda Ya haliccesu tun afarko da ba su, sai ya yi musu raddi da cewa Wanda Ya fari halitta daga babu mai iko ne akan dawo dasu kai hakan mafi sauki ne ma, duk da al'amarin dangane da Allah daidai ne halitta da dawowa, Allah Mai iko ne akan dukkan komai. Amma aibantawar: To fadinsu: Cewa Shi Yana da Da, sai ya yi musu raddi da cewa Shi ne daya Kwal, Mai kadaituwa da dukkanin cika a sunayenSa da siffofinSa da ayyukanSa, abin tsarkakewa daga kowacce tawaya da aibi, abin nufi da bukata wanda baYa bukatuwa ga wani, kuma kowa mai bukatuwane gareShi, kuma bai zama mahaifi ga wani ba, kuma baShi da wani Da, kuma baShi da tamka, tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka.

فوائد الحديث

Tabbatar da cikar iko ga Allah - Madaukakin sarki -.

Tabbatar da tashi bayan mutuwa.

Kafircin wanda ya musanta tashi bayan mutuwa ko ya danganta Da ga Allah - Madaukakin sarki -.

Babu tamka ko kini ga Allah - Madaukakin sarki -.

Yalwar hakurin Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, da jinkirtawarSa ga kafirai watakila su zasu tuba su koma.

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi