mafi arzikin mutane da cetona a ranar Kiyama, wanda ya ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana mai tsarkakewa daga zuciyarsa ko ransa

mafi arzikin mutane da cetona a ranar Kiyama, wanda ya ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana mai tsarkakewa daga zuciyarsa ko ransa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Aka ce ya Manzon Allah waye mafi azirtar mutane da cetanka a ranar Kiyama? Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Hakika ya Abu Huraira na yi zatan babu daya da zai tambayeni game da wannan hadisin na farko daga kai, saboda abinda na gani na kwadayinka akan hadisi, mafi arzikin mutane da cetona a ranar Kiyama, wanda ya ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana mai tsarkakewa daga zuciyarsa ko ransa".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa mafi azirtar mutane da cetansa a ranar alkiyama shi ne wanda ya ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana mai tsarkakewa daga zuciyarsa". Wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ya zama kubutacce daga shirka da riya.

فوائد الحديث

Tabbatar da ceto ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a lahira, kuma cewa shi ceton ba ya kasancewa sai ga masu Tauhidi.

Cetonsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne tawassalinsa zuwa ga Allah - Madaukakin sarki - ga wanda ya cancanci shiga wuta daga masu Tauhidi cewa ba zai shigeta ba, wanda kuma ya shiga wutar da cewa zai fita daga cikinta muddin yana da Tauhidi.

Falalar kalmar Tauhidi tsarkakkiyya ga Allah - Madaukakin sarki - da kuma girman tasirinta.

Tabbatar da kalmar Tauhidi yana kasancewa ne da sanin ma'anarta, da kuma aiki da abinda taka kunsa.

Falalar Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - da kuma kwadayinsa akan ilimi.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya