Mafi tsananin azaba a wurin Allah a ranar Alkiyama wadanda suke kwaikwayon halittar Allah

Mafi tsananin azaba a wurin Allah a ranar Alkiyama wadanda suke kwaikwayon halittar Allah

Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo wurina, hakika na rufe jarkata da wani labule a jikinsa akwai hotuna, lokacin da ya gan shi sai ya yaye shi, fuskarsa ta janza ya ce : "Ya A'isha, Mafi tsananin azaba a wurin Allah a ranar Alkiyama wadanda suke kwaikwayon halittar Allah" A'isha ta ce: "Sai muka yanke shi sai muka maida shi shinfida ko shinfidu biyu".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga dakinsa ga A'isha - Allah Ya yarda da ita - sai ya sameta ta rufe jarkarta karama wacce take sanya kayanta a ciki da wani yanki a jikinsa akwai hotunan masu rayuka, sai launin fuskarsa ya canja dan fushi saboda Allah sai ya cire shi, ya ce: Mafi tsananin azaba a ranar Alkiyama wadanda suke kamanta halittar Allah da hotunansu. A'isha ta ce: sai muka maida shi shinfida ko shinfidu biyu.

فوائد الحديث

Hana abin ki a lokacin ganinsa da rashin jinkiri a hakan, muddin dai babu wata barna mafi girma a hakan.

Azabar ranar Alkiyama tana banbanta a tsanani gwargwadan girman zunubi.

Yin hoton abubuwa masu rai yana daga manyan zanubai.

Yana daga hikimomin haramta hoto kamanceceniya da halittar Allah - Madaukakin sarki -, duk daya ne mai hoton ya yi nufin kamanceceniya ne ko bai yi nufi ba.

Kwadayin shari'a akan kiyaye dukiyoyi ta hanyar fa'idantuwa daga gare su bayan an nisantarsu abinda ya haramta a cikinsu.

Hani akan kera zanen abubuwa masu rai akan kowanne yanayi ya kasance, koda sun kasance a wulakance ne.

التصنيفات

Tauhidin Rububiyya, Tauhidin Rububiyya