Lallai Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Zai cewa 'yan aljanna: Yaku 'yan aljanna? sai su ce: AmsawarKa ya Ubangijinmu da dai amsawarKa, sai Ya ce: Shin kun yarda? Sai su ce: Dan me ba zamu yarda ba alhali Ka bamu abinda baKa bawa wani daga halittarKa ba?

Lallai Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Zai cewa 'yan aljanna: Yaku 'yan aljanna? sai su ce: AmsawarKa ya Ubangijinmu da dai amsawarKa, sai Ya ce: Shin kun yarda? Sai su ce: Dan me ba zamu yarda ba alhali Ka bamu abinda baKa bawa wani daga halittarKa ba?

Daga Abu Sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Zai cewa 'yan aljanna: Yaku 'yan aljanna? sai su ce: AmsawarKa ya Ubangijinmu da dai amsawarKa, sai Ya ce: Shin kun yarda? Sai su ce: Dan me ba zamu yarda ba alhali Ka bamu abinda baKa bawa wani daga halittarKa ba? Sai Ya ce: Ni zan baku mafifici daga hakan, sai su ce: Ya Ubangiji, wane abu ne maffifici daga hakan? Sai Ya ce: Zan saukar muku da yardata, ba zan yi fushi daku ba a bayansa har abada".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - zai cewa 'yan aljanna alhali su suna cikinta: Yaku 'yan aljanna, sai su amsa maSa suna masu cewa: AmsawarKa ya Ubangijinmu da dai amsawarKa, Sai Ya ce musu: Shin kun yarda? sai su ce: Eh mun yarda; Danme ba zamu yardaba alhali ka bamu abinda baKa bawa wani daga halittarka ba! Tsarki ya tabbatar maSa Zaice: Shin ba zan baku mafifici daga hakan ba? Sai su ce: Wane abu ne mafifici daga hakan?! Sai ya ce: Zan saukar muku dawwamammiyar yarda ta; ba zan yi fushi daku a abayanta ba har abada.

فوائد الحديث

Zancen Allah - Mai girma da ɗaukaka - tare da 'yan aljanna.

Albishir daga Allah ga 'yan aljanna da yardarSa garesu, da saukar da yardarSa garesu, da rashin fushinSa har abada.

Yardar duk wani ɗan aljanna da yanayin halinsa tare da saɓanin matsayinsu da banbancin darajojinsu; domin dukkaninsu sun amsa da lafazi ɗaya shi ne: "Ka bamu abinda baka bawa wani daga halittarka ba".

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi, Sifar Al-janna da Wuta