Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona

Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana cewa: Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona, idan ya ambaceNi a cikin ransa zan ambace shi a cikin raiNa, idan ya ambaceni a cikin mutane zan ambace shi a cikin mutanen da suka fisu alheri, idan ya kusantoNi taki (ɗaya), Zan kusanto zuwa gare shi zira'i (ɗaya), idan ya kusanto zuwa gareNi zira'i (ɗaya), zan kusanto gare shi faɗin hannaye, idan ya zo miNi yana tafiya zan zo masa ina gaggawa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana cewa: Ni ina inda zatan bawaNa gareNi yake, zan yi mu'amala da bawaNa gwargwadan zatansa da Ni, hakan dan ƙauna da burin rangwami, kuma Ina yi masa abinda yake tinanin afkuwarsa daga gareNi na alheri ne ko wanin hakan; kuma Ni ina tare da shi da rahama da dacewa da shiriya da kiyayewa da ƙarfafawa idan ya anbaceNi. Idan ya anbaceNi a cikin ransa shi kaɗai a kaɗaice da tasbihi da hailala ko waninsu; zan anbace shi a cikin raiNa. Idan ya anbaceNi a cikin jama'a; zan ambace shi a cikin jama'ar da tafisu yawa kuma ta fisu tsarki. Wanda ya nemi kusanci zuwa ga Allah gwargwadan taki Allah Zai yi masa ƙari sai Ya kusanto zuwa gare shi da zira'i. Idan ya nemi kusanci zuwa gare shi gwargwadan zira'i zai kusanto zuwa gare shi gwargwadan awon faɗin hannaye. Idan ya zo zuwa ga Allah yana tafiya to Allah zai zo masa Yana sassarfa. Bawa idan ya nemi kusanci zuwa ga Ubangijinsa da biyayya gareShi da fuskantowa gareShi, to lallai Ubangiji - Maɗaukakin sarki - Zai ƙara kusanci zuwa gareshi dan sakamako daga jinsin aikinsa. A duk lokacin da bautar mumini ta cika ga Ubangijinsa to Allah Maɗaukakin sarki zai kusanto zuwa gare shi, kyautar Allah da sakamakonSa (ita ce ) mafi yawa daga aikin bawa da kuma wahalarsa, a taƙaice cewa sakamakon Allah mai rinjaya ne akan aiki ta hanyar kaifiyya da kuma kimmiya. Mumini yana kyautata zato, kuma yana aiki, yana gaggawa yana ƙarawa har ya gamu da Allah.

فوائد الحديث

Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu keɓance-keɓancen AlƘur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninSa, kamar bauta da karanta shi, da yin tsarki sabo da shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.

Al-Aajurri ya ce: Lallai ma'abota gaskiya suna siffanta Allah - Mai girma da ɗaukaka - da abinda Ya siffanta kanSa - Mai girma da ɗaukaka - da shi, da kuma abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta shi da shi, kuma da abinda sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka siffantaShi da shi, wannan (ita ce) mazhabar malamai daga waɗanda ya bi bai yi ƙirƙire ba, Ya ƙare.

Ahlus Sunna suna tabbatarwa Allah abinda Ya tabbatarwa kanSa da shi na sunaye da siffofi ba tare da jirkitawa ko korewa ko kaifantawa ko kamantawa ba, kuma suna korewa Allah abinda Ya korewa kanSa, sunayin shiru daga abinda korewa ko tabbatarwa bai zo da shi ba, Allah - madaukakin sarki - ya ce: {Babu wani abu tamkarSa, Shi ne Mai yawan ji kuma Mai yawan gani}.

Kyautata zato ga Allah babu makawa daga aiki a tare da shi, al-Hasanul Basri ya ce: Lallai cewa mumini ya kyautata zato ga Ubangijinsa sai ya kyautata aiki, kuma lallai cewa fajiri ya munana zato ga Ubangijinsa sai ya munana aiki.

Al-Ƙurɗubi ya ce: An ce: Ma'anar "Zaton bawaNa gareNi" Zaton amsawa a yayin addu'a, da kuma zatan karɓa a yayin tuba, da zatan gafara a yayin istigfari, da zatan sakayya a yayin aikin ibada da sharuɗɗanta dan riƙo da gaskiyar alƙawarinsa, saboda haka yana kamata ga mutum ya yi ƙoƙari a tsayuwa da abinda ke kansa yana mai sakankancewa da cewa Allah Zai karɓe shi kuma Ya gafarta maSa; domin cewa shi ya yi alƙawari da hakan kuma Shi baYa saɓa alƙawari, idan ya ƙudirce ko ya yi zaton cewa Allah ba Zai karɓeta ba ko kuma cewa ba zata anfane shi ba to wannan shi ne yanke ƙauna daga rahamar Allah, kuma hakan yana daga manyan laifuka, wanda ya mutu akan hakan za'a wakilta shi zuwa abinda ya yi zato kamar yadda yake cikin sashin hanyoyin hadisin da aka anbata; "To bawaNa ya yi zato Na da abinda ya so", ya ce: Amma zatan gafara tare da nacewa akan sabo to hakan shi ne tsantsar jahilci da ruɗuwa.

Kwaɗaitarwa akan yawaita anbatan Allah a cikin ranka da harshenka gaba ɗaya, yana jin tsoron Allah a cikin ransa da zuciyarsa ya dinga tuna girmanSa da haƙƙinSa ya ƙaunace Shi ya girmamaShi ya so Shi ya kyautata masa zato ya tsarkake aiki, ya furta da harshe: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, babu wata dabara babu wani ƙarfi sai ga Allah.

Ibnu Abi Jamrah ya ce: Wanda ya anbace shi alhali shi yana mai jin tsoro zai amintar da shi, ko mai kewa zai ɗebe masa kewa.

Taki: (shi ne) faɗin dake tsakanin ƙaramin ɗan yatsa zuwa babban ɗan yatsa a yayin miƙe tafi.

Zira'i kuwa: (shi ne) faɗin dake tsakanin gefen ɗan yatsa na tsakiya har zuwa ƙashin gwiwar hannu.

Ba'i kuwa: (Shi ne) tsawon zira'i biyu na mutum da kuma damattsansa da faɗin ƙirjinsa; hakan (shi ne) gwargwadan zira'i huɗu.

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi, Fa’idojin Ambaton Allah Maigirma da xaukaka