Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna, wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta

Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna, wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, wadanne abu biyu ne masu wajabtawa? Sai ya ce: "Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna, wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta"

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da dabi'u biyu: Wacce take wajabta shiga Aljanna, da wacce take wajabta shiga wuta? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya amsa masa: Cewa dabi'ar da take wajabta Aljanna ita ce mutum ya mutu alhali yana bautawa Allah Shi kadai ba ya taranya wani abu da shi, Kuma cewa dabi'ar da take wajabta wuta ita ce mutum ya mutu alhali shi yana taranya wani abu da Allah, sai ya sanya kishiya ga Allah da tamka a cikin AllantakarSa ko a kasancewar shi ne Mahalicci ko sunayenSa da siffofinSa.

فوائد الحديث

Falalar Tauhidi da cewa wanda ya mutu yana mumini ba ya taranya Allah da wani abu zai shiga Aljanna.

Hadarin shirka, cewa wanda ya mutu yana taranya Allah da wani abu zai shiga wuta.

Masu Tauhidi wadanda suke sabo suna karkashin ganin damar Allah, in Ya so Ya azabtar da su, idan ya so Ya gafarta musu, sannan makomarsu tana ga Aljanna.

التصنيفات

Imani da Allah Maxaukaki, Tauhidin Uluhiyya, Falalar Tauhidi