إعدادات العرض
1- Babu wani Musulmi da wata Wahala zata Same shi, ko rashin lafiya, Ko Damuwa ko Bacin rai, ko wata Cuta ko Damuwa, kai Har Kaya da zai taka ta face sai allah ya Kankare masa Zunubansa da ita
2- Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne da gaske daga zuciayarsa sai wuta ta haramta a gareshi
3- Lalle cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa kada su hada shi komai, hakkin bayi ga Allah ba zai azabtar da wanda bai tarayya daShi da komaiba
4- Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna, wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta
5- Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'ummata agaban halittu a ranar Alkiyama
6- Kada ku dauki kabarina a matsayin idi, haka kuma gidajenku ba su zama kaburbura ba, ku yi min addu’a, saboda mika wuyan ku ya fada min inda kuka kasance
7- Ya Manzon Allah, ban bar wata karamar bukata ko babba ba sai da na zo mata, (na laifi) ya ce: "Shin baka kasance kana shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba kuma cewa Muhammad Manzon Allah ne?
8- Ayyuka shida ne, mutane kuma hudu ne, akwai tabbatattu biyu. Da tamka da tamka, da kyakkyawa da tamkarta goma, da kyakkyawa da dari bakwai
9- Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, zan yi maka shaida da ita ranar Alkiyama