Ya Manzon Allah, ban bar wata karamar bukata ko babba ba sai da na zo mata, (na laifi) ya ce: "Shin baka kasance kana shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba kuma cewa Muhammad Manzon Allah ne?

Ya Manzon Allah, ban bar wata karamar bukata ko babba ba sai da na zo mata, (na laifi) ya ce: "Shin baka kasance kana shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba kuma cewa Muhammad Manzon Allah ne?

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, ban bar wata karamar bukata ko babba ba sai da na zo mata, (na laifi) ya ce: "Shin baka kasance kana shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba kuma cewa Muhammad Manzon Allah ne?" Sau uku. ya ce: Eh, ya ce: "Lallai hakan zai zo akan hakan (wato zai rufe shi )".

[Ingantacce ne]

الشرح

Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa ni hakika na aikata dukkanin zunubai da sabo, ban bar wani karamin laifi ba ko babba sai da na aikata shi , shin za'a gafarta mini? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: Shin baka shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba ?? kuma Muhammad Manzon Allah ne? Ya maimaita masa sau uku. Sai ya amsa masa: Eh ina shaidawa, Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata gare shi - ya ba shi labarin falalar shahada biyu, da kuma kankarewarta ga munanan laifuka, kuma lallai cewa tuba yana kankare abinda ke kafinsa.

فوائد الحديث

Girman (Kalmar) shahada biyu da kuma rinjayarta akan zunubai ga wanda ya fadeta yana mai gaskiya daga zuciyarsa.

Musulunci yana kankare abinda ke kafinsa.

Tuba na gaskiya yana shafe abinda ke kafinsa.

Maimaitawa a cikin ilimantarwa yana daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Falalar (Kalmar) shahada biyu, kuma cewa su sababi ne na tsira daga dawwama a cikin wuta.

التصنيفات

Falalar Tauhidi