Ba abinda yake samun musulmi na wahala ko rashin lafiya ko bakin ciki ko takaici ko cuta ko bakin ciki har kayar da zai taka, sai Allah ya kankare masa kurakuransa da su

Ba abinda yake samun musulmi na wahala ko rashin lafiya ko bakin ciki ko takaici ko cuta ko bakin ciki har kayar da zai taka, sai Allah ya kankare masa kurakuransa da su

Daga Abu Sa'id Alkhudri da Abu Hurarira - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ba abinda yake samun musulmi na wahala ko rashin lafiya ko bakin ciki ko takaici ko cuta ko bakin ciki har kayar da zai taka, sai Allah ya kankare masa kurakuransa da su".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa abinda musulmi yake samu na cutuka da bakin cki da takaici da masibu da tsanani da tsoro da yunwa - kai koda akwai kayar da za ta taba shi ta sashi radadi -, hakan zai zama kaffara ga zunubansa da kuma kankare kurakuransa.

فوائد الحديث

Bayanin falalar Allah ga bayinSa muminai da kuma rahamarSa garesu ta hanyar gafarta zunubai da mafi karancin cutar da zata samesu.

Ya kamata ga musulmi ya nemi ladan abinda ya sameshi a wurin Allah, ya kuma yi hakuri akan dukkanin karami da babba, dan ya zama yana samun daukakar darajoji da kuma kankarewa ga munanan laifuka.

التصنيفات

Falalar Tauhidi