إعدادات العرض
Duk wanda ya gamu da Allah ba ya hada wani abu da shi to kuskurensa ba zai cutur da shi tare da shi ba, wanda kuwa ya mutu alhali yana yin shirka da shi wani kyakkyawan aikinsa ba zai amfane shi tare da shi da komai ba
Duk wanda ya gamu da Allah ba ya hada wani abu da shi to kuskurensa ba zai cutur da shi tare da shi ba, wanda kuwa ya mutu alhali yana yin shirka da shi wani kyakkyawan aikinsa ba zai amfane shi tare da shi da komai ba
Daga Abdullahi Ibnu Amr Ibnul Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ya gamu da Allah ba ya hada wani abu da shi to kuskurensa ba zai cutur da shi tare da shi ba, wanda kuwa ya mutu alhali yana yin shirka da shi wani kyakkyawan aikinsa ba zai amfane shi tare da shi da komai ba"
[Ingantacce ne] [Ahmad ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية Português دری Македонски Magyar Tiếng Việt ქართული Kurdî বাংলা ไทย অসমীয়া Nederlands ਪੰਜਾਬੀ Bahasa Indonesia Kiswahili ភាសាខ្មែរ English ગુજરાતીالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya mutu kuma ya gamu da Allah yana mai kaɗaita Allah ba ya hada wani da abu da shi to shi yana daga cikin 'yan aljanna, ko da an yi masa uƙuba da zunubinsa a cikin wuta. Wanda ya mutu alhali yana hada wani abu da shi to wani kyakkyawan aiki ba zai yi amfani tare da shirkarsa ba; kuma aljanna haramun ce gare shi .فوائد الحديث
Gargaɗarwa daga shirka, kuma cewa ita ce mafi girman zunubai da kurakurai, kuma cewa Allah baYa gafarta ta.
Falalar tauhidi, kuma shi Tauhidi yana wajabta shiga aljanna; ko da bayan an yi azaba ne.
Muhimmancin tabbata akan tauhidi har zuwa mutuwa, da kuma rashin aikata kishiyarsa na shirka.
