Lalle cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa kada su hada shi komai, hakkin bayi ga Allah ba zai azabtar da wanda bai tarayya daShi da komaiba

Lalle cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa kada su hada shi komai, hakkin bayi ga Allah ba zai azabtar da wanda bai tarayya daShi da komaiba

Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance a bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wani jaki ana ce masa Ufair, sai ya ce: "Ya Mu'az, shin kasan hakkin Allah akan bayin Sa, kuma menene hakkin bayi ga Allah?", sai na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "Lalle cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa kada su hada shi komai, hakkin bayi ga Allah ba zai azabtar da wanda bai tarayya daShi da komaiba", sai na ce: Ya Manzon Allah shin ba nayiwa mutane albishir da shi ba? Ya ce: "Kada ka yi musu albishir, sai su dogara".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana hakkin Allah akan bayi, da hakkin bayi ga Allah, lallai cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa Shi kadai kada su hada shi da wani abu. Kuma cewa hakkin bayi ga Allah shi ne ba zai azabtar da masu kadaitaShi da bauta ba, wadanda ba sa sanya masa abokin tarayya ba. Sannan cewa Mu'az, ya ce: Ya Manzon Allah, shin baa a yi wa mutane albishir da shi ba dan su yi farinciki, kuma su yi murna da wannan falalar ba ?? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana shi dan tsoron kada su dogara akanta.

فوائد الحديث

Bayanin hakkin Allah - madaukakin sarki - wanda ya wajabta shi akan bayinSa, shi ne su bauta maSa, kada su hada da komai.

Bayanin hakkin bayi ga Allah - madaukakin sarki - wanda Ya wajabtaShi akan kanSa dan falala daga gareShi da kuma ni'ima, shi ne Ya shigar da su Aljanna, kada ya azabtar da su.

A cikinsa akwai albishir mai girma ga masu kadaita Allah wadanda ba sa taranya wani abu daShi da cewa makomarsu (ita ce) shiga Aljanna.

Mu'azu ya karantar da wannan Hadisin kafin mutuwarsa; dan tsoron fadawa a cikin zunubin boye ilimi.

Fadakarwa akan rashin yada sashin Hadisai ga wasu mutane dan tsoron kada wanda bai riski ma'anarsuba; wannan a cikin abinda a karkashinsa babu wani aiki, kuma babu wani haddi daga haddodin Shari’a..

Masu kadaita Allah masu sabo suna karkashin ganin damar Allah, in Yaso ya yi musu azaba, idan kuma Yaso Ya gafarta musu, sannan makomarsu tana ga Aljanna.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya, Falalar Tauhidi