Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, zan yi maka shaida da ita ranar Alkiyama

Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, zan yi maka shaida da ita ranar Alkiyama

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - ya cewa Baffansa; "Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, zan yi maka shaida da ita ranar Alkiyama", ya ce: Da badan Kuraishawa zasu aibatani ba, zasu ce: Razani da tsoron mutuwa ne suka kai shi haka ba da na faranta ranka da ita. Sai Allah Ya saukar: {Lallai kai ba zaka shiryar da wanda ka so ba saidai Allah Yana shiryar da wanda yake so} [Al-Kasas; 56].

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nema daga baffansa Abu Dalib alhali shi yana magagin mutuwa da ya furta; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan ya cece shi da ita ranar Alkiyama , kuma ya yi masa shaidar Musulunci, sai yaki furta shaidar dan tsoron kada Kuraishawa ta zargeshi ta ce da shi: Cewa shi ya musulunta ne saboda tsoron mutuwa da rauni! sai ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi: Da badan haka ba da na shigar da farin ciki a zuciyarka da furta shaidar, na isar da burinka har ka yarda! sai Allah Ya saukar da ayar da take nuni akan cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya mallakar shiriya ta dacewa da Musulunci, kawai Allah - Mai girma da daukaka -Shi kadai ne Yake datar da wanda Yake so. Kuma Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -yana shiryar da halitta ta shiryarwa da bayani da kira zuwa hanya madaidaiciya.

فوائد الحديث

Ba'a barin gaskiya dan tsoro daga zancen mutane.

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kadai yana mallakar shiriyar nuni ne da fadakarwa kawai ba shiriyar dacewa ba.

Halaccin ziyarar kafiri mara lafiya dan kiransa zuwa ga Musulunci.

Kwadayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan kira zuwa ga Allah - Madaukakin sarki - a kowane hali.

التصنيفات

Imani da Hukuncin Allah da Qaddara, Abubuwan da suke warware Musulunci, Falalar Tauhidi