Kada ku ce : Allah Ya so wane ma ya so, saidai ku ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so

Kada ku ce : Allah Ya so wane ma ya so, saidai ku ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so

Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku ce : Allah Ya so wane ma ya so, saidai ku ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so".

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya ce a zancensa: Allah Ya so wane ma ya so", ko Allah Ya so da wane; hakan domin ganin damar Allah da nufinSa a wawaice suke, wani ba ya tarayya daShi a cikinsu, a cikin amfani da Waw (da) a adafi alamtarwa ne na hada wani tare da Allah da daidaitawa a tsakaninsu. Saidai ya ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so, Sai ya sanya ganin damar bawa mai bi ce ga ganin damar Allah ta hanyar fadin: "Sannan" canjin "da"; domin "sannan" tana fa'idantar da bibiya da kuma jinkiri.

فوائد الحديث

Haramcin fadin: "Allah Ya so kaima ka so" da makamancin hakan daga lafazukan da acikinsu akwai adafi ga Allah da Waw; domin cewa shi yana daga Shirka ta lafazi da maganganu.

Halaccin fadin: "Allah ne Ya so sannan ka so", da abinda ke kama da hakan daga abinda a cikinsa akwai adafi ga Allah da Summa (sannan); dan koruwar abinda ake gudu a cikinsa.

Tabbatar da ganin damar Allah, da kuma ganin damar bawa, kuma cewa Mashi'ar bawa mai bi ce ga Mashi'ar Allah - Madaukakin sarki -.

Hani daga tarayya da halitta a cikin Mashi'ar Allah koda da lafazi ne.

Idan mai fada ya kudirce cewa Mashi'ar bawa kamar Mashi'ar Allah ce - Mai girma da daukaka - daidai da ita a gamewa da wawaita, ko cewa bawa yana da Mashi'a tsayayya to wannan babbar shirka ce, amma idan ya kudire cewa shi koma bayansa ne; to shirka ce karama.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya