Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya maida makircinsa zuwa wasiwasi

Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya maida makircinsa zuwa wasiwasi

Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo gurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai dayanmu yana ji aransa - ana bijiro masa da abu - ya zama toka shi ya fi masa da ya fadi maganar, sai ya ce: "Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya maida makircinsa zuwa wasiwasi".

[Ingantacce ne]

الشرح

Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai dayanmu yana jin wani al'amari yana bijiro masa a zuciyarsa, saidai ya fade shi abu ne mai girma ne wanda ya kai matakin ace ya zama toka ya fi soyuwa agare shi akan ya fadeta. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi kabbara sau biyu ya godewa Allah da ya mayar da kaidin Shaidan zuwa ga mujarradin wasuwasi.

فوائد الحديث

Bayanin cewa Shaidan yana dakon muminai da wasuwasi; dan ya juyar da su daga imani zuwa kafirci.

Bayanin raunin Shaidan game da ma'abota imani yayin da bai samu wani iko ba sai wasiwasi kawai.

Yana kamata ga mumini ya bijirewa wasiwasin Shaidan da kuma tunkude shi.

Halaccin kabbara yayin wani abu abin so ko mamaki, daga gareshi ko mai kama da shi daga al'amaura.

Halaccin tambayar musulmi ga malami game da dukkanin abinda yake rikitar da shi.

التصنيفات

Imani da Allah Maxaukaki, Aljanu