Lallai Allah - mai girma da daukaka - yana hanaku ku rantse da iyayenku

Lallai Allah - mai girma da daukaka - yana hanaku ku rantse da iyayenku

Daga Umar Dan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah - mai girma da daukaka - yana hanaku ku rantse da iyayenku", Umar ya ce: Na rantse da Allah ban yi rantsuwa da su ba tunda na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga garesu da gangan ko ina mai ciratowa (daga wanina).

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Madaukakin sarki - Yana hani daga rantsuwa da iyaye, duk mai nufin yin rantsuwa kada ya rantse da kowa sai da Allah, kada ya rantse da waninsa. Sannan Umar Dan Khaddab - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa shi bai sake rantsuwa da su ba tunda ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani game da hakan, bada gangan ba, ba kuma yana mai cirato rantsuwa da wanin Allah daga waninsa ba.

فوائد الحديث

Haramcin rantsuwa da wanin Allah, an kebanci rantsuwa da iyaye; domin ita tana daga al'adun Jahiliyya.

Rantsuwa: Ita ce rantsuwa da Allah ko da sunayen Allah ko da siffofin Allah akan wani al'amari daga al'amura dan karfafashi.

Falalar Umar - Allah Ya yarda da shi - da gaggauta barin abinda aka hana da kyakkyawan fahimtarsa da kuma tsantseninsa.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya