إعدادات العرض
Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Allah kuma kada ku sanya wa Allah wani abun tarayya da Shi, da salloli biyar, ku bi - sai ya boye wata kalma boyayya - kada ku tambayi mutane komai
Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Allah kuma kada ku sanya wa Allah wani abun tarayya da Shi, da salloli biyar, ku bi - sai ya boye wata kalma boyayya - kada ku tambayi mutane komai
Daga Abu Muslim Al-Khaulani ya ce: Masoyi amintacce ya zantar dani, amma shi to masoyi ne gareni, amma shi a wajena to amintaccene, Awf Dan Malik Al-Ashja'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - (Mu) tara ko takwas ko bakwai, sai ya ce: "Shin ba kwa yi wa Manzon Allah caffa ba?" mun kasance farkon yin caffa (mubaya’a) sai muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, sannan ya ce: "Shin bakwa yi wa Manzon Allah caffa ba?" sai muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, sannan Ya ce: "Shin bakwa wa Manzon Allah caffa ba?" Ya ce: Sai muka shimfida hannayenmu muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Allah kuma kada ku sanya wa Allah wani abun tarayya da Shi, da salloli biyar, ku bi - sai ya boye wata kalma boyayya - kada ku tambayi mutane komai" Hakika na ga sashin wadancan mutanan bulalar dayansu tana faduwa, amma ba ya tambayar wani ya miko masa.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල Kurdî Kiswahili Português Русский Svenska ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá ئۇيغۇرچە پښتو অসমীয়া دری Кыргызча or Malagasy नेपाली Čeština Oromoo Română Nederlands Soomaali తెలుగు മലയാളം Српски ไทย mr Kinyarwanda ಕನ್ನಡ Lietuvių Shqip Wolofالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin wani adadi na sahabbai sai ya nemi su yi masa caffa su yi masa alkawari akan lazimtar wasu al'amura har sau uku: Na farko: Bautar Allah Shi kadai ta hanyar riko da umarninSa, da nisantar haninSa, kuma kada su hada wani abu daShi. Na biyu: Tsaida salloli biyar na wajibai a yini da dare. Na uku: Ji da bi da aikin alheri ga wanda ya jibinci al'amarin musulmai. Na hudu: Kai dukkanin bukatunsu ga Allah da rashin tambayar mutane wani abu daga garesu, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi kasa-kasa da sautinsa da su. Hakika sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun yi aiki da abinda suka yi caffa akansa, har maruwaicin Hadisin ya ce: Hakika na ga wasu daga wadancan sahabban bulalar dayansu tana faduwa kasa , amma ba ya tambayar wani ya miko masa ita, kai yana sauka yana daukarta da kansa.فوائد الحديث
Kwadaitarwa akan barin tambayar mutane, da tsarkaka daga dukkanin abinda ake kira tambaya, da wadatuwa daga mutane koda a wani al'amari kankani ne.
Tambayar da aka hana: Tambaya mai alaka da al'amura na duniya, ba ta hado tambaya game da ilimi da al'amuran Addini ba.
التصنيفات
Tauhidin Uluhiyya