Wanda ya rataya laya to haƙiƙa ya yi shirka

Wanda ya rataya laya to haƙiƙa ya yi shirka

Daga Uƙuba ɗan Amir Aljuhani - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane sun fuskanto gare shi , sai ya yi wa tara daga cikinsu caffa (Mubaya’a) yaki yi wa ɗaya, sai suka ce: Ya Manzon Allah, ka yi wa tara caffa ka bar wannan? ya ce: "Atare da shi akwai laya". Sai ya shigar da hannunsa sai ya yanketa, sai ya yi masa caffa, ya ce: "Wanda ya rataya laya to haƙiƙa ya yi shirka".

[Ingantacce ne] [Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Wasu jama'a sun zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, adadinsu su goma ne, sai ya yi Mubaya’awa tara daga cikinsu (Wato caffa) akan Musulunci da bi, bai yi wa na goman ba, yayin da aka tambaye shi game da sababin hakan sai tsira da amincin su tabbata agare shi ya ce: Lallai atare da shi akwai laya, ita ce abinda ake ɗaurawa ko ake ratayawa na laya (guru ko kamun) ko waninsa don tunkuɗe kanbun baka ko wata cuta. Sai mutumin ya shigar da hannunsa gurin layar ya yanketa ya kuɓuta daga gareta, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa caffa, ya ce yana mai gargaɗarwa daga layu yana mai bayyana hukuncinsu: "Wanda ya rataya laya to haƙiƙa ya yi shirka".

فوائد الحديث

Wanda ya dogara ga wanin Allah, Allah Zai yi masa mu'amala da saɓanin nufinsa.

Kudirce cewa rataya layu sababi ne na tunkuɗe cuta da kanbun baka to ƙaramar shirka ce, amma idan ya ƙudirce cewa suna amfanarwa da kansu to hakan babbar shirka ce.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya