Lallai Allah Ya rubuta kyawawa (lada) da munana (alhaki), sannan Ya bayyana hakan, wanda ya yi nufin kyakkyawa bai aikatata ba, to, Allah zai rubuta masa kykkyawa cikakkiya, idan ya yi nufinsa sai ya aikatata, to, Allah Zai rubuta masa kyawawa goma a wurinsa zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da…

Lallai Allah Ya rubuta kyawawa (lada) da munana (alhaki), sannan Ya bayyana hakan, wanda ya yi nufin kyakkyawa bai aikatata ba, to, Allah zai rubuta masa kykkyawa cikakkiya, idan ya yi nufinsa sai ya aikatata, to, Allah Zai rubuta masa kyawawa goma a wurinsa zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, wanda ya yi nufin mummuna bai aikatashi ba, to, Allah Zai rubuta kykkyawa cikakke, idan ya yi nufinsa sai ya aikatashi Allah Zai rubuta masa mummuna ɗaya

Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin abin da yake ruwaitowa daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - ya ce: Ya ce: "Lallai Allah Ya rubuta kyawawa (lada) da munana (alhaki), sannan Ya bayyana hakan, wanda ya yi nufin kyakkyawa bai aikatata ba, to, Allah zai rubuta masa kykkyawa cikakkiya, idan ya yi nufinsa sai ya aikatata, to, Allah Zai rubuta masa kyawawa goma a wurinsa zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, wanda ya yi nufin mummuna bai aikatashi ba, to, Allah Zai rubuta kykkyawa cikakke, idan ya yi nufinsa sai ya aikatashi Allah Zai rubuta masa mummuna ɗaya".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah Ya ƙaddara kyawawa da munana, sannan Ya bayyanawa Mala'iku biyu yaya zasu rubuta su: Wanda ya yi nufi a kan aikata kykkyawa za'a rubuta masa kyakkyawa ɗaya ko da bai aikatashi ba, idan ya aikatashi, to, za a ninkashi da tamkarsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, ƙarin yana kasancewa ne da gwargwadan abin da ke cikin zuciya na ikhlasi da ƙetarewar amfani da makamancin hakan. Wanda ya yi nufin aikata mummuna sannan ya barshi saboda Allah, za a rubuta masa kykkyawa, idan ya barshi don shagaltuwa da barinsa, tare da rashin aikata sabubbanta ba za a rubuta masa komai ba, idan ya barshi don gajiyawa daga gareshi za a rubuta masa niyyarsa, idan ya aikatata za a rubuta masa mummuna ɗaya.

فوائد الحديث

Bayanin falalar Allah mai girma ga wannan al'ummar wajen ninka kyawawa da kuma rubutasu a wurinsa, da rashin ninka munana.

Muhimmancin niyya a cikin ayyuka da kuma tasirinta.

Falalar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da saukinsa da kyutatawarsa cewa wanda ya yi nufin kyakkywa bai aikatashi ba, to, Allah Zai rubutashi a matsayin kykkyawa.

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi