Ku kusanto ku daidaita, ku sani cewa babu wani daga cikinku da zai tsira da aikinsa". Suka ce: Ya Manzon Allah koda kaine?ya ce: "Koda nine sai dai idan Allah Ya lulluɓeni da rahamarSa da kuma falalarSa

Ku kusanto ku daidaita, ku sani cewa babu wani daga cikinku da zai tsira da aikinsa". Suka ce: Ya Manzon Allah koda kaine?ya ce: "Koda nine sai dai idan Allah Ya lulluɓeni da rahamarSa da kuma falalarSa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku kusanto ku daidaita, ku sani cewa babu wani daga cikinku da zai tsira da aikinsa". Suka ce: Ya Manzon Allah koda kaine?ya ce: "Koda nine sai dai idan Allah Ya lulluɓeni da rahamarSa da kuma falalarSa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da sahabbai akan su yi aiki, kuma su ji tsoron Allah gwargwadan ikonsu, ba tare da zurfafawa ko Gazawa ba, kuma su nufi daidai da aikinsu ta hanyar ikhlasi ga Allah da bin sunna dan a karɓi aikinsu sai su zama sababi ga saukar rahama garesu. Sannan ya ba su labarin cewa wani mutum aikinsa kawai ba zai tseratar da shi ba; kai babu makawa daga rahamar Allah. Suka ce: Har kai Ya Manzon Allah aikinka ba zai tseratar da kai ba tare da girman darajarsa? Sai ya ce: Har ni, sai dai in Allah Ya suturtani da falalar rahamarSa.

فوائد الحديث

AlNawawi ya ce: (Ku daidaita ku kusanto): Ku nemi daidai, kuma ku yi aiki da shi ko da kun gajiya daga hakan, to ku kusanto gare shi; wato: Ku kusanto gare shi, daidai; (shi ne) daidai, shi ne tsakanin wuce gona da iri da kuma sakaci, kada ku zurfafa kuma kada ku yi sakaci.

Ibnu Baz ya ce: Ayyuka na gari su ne sabubban shiga aljanna, kamar yadda munanan ayyuka su ne sabubban shiga wuta, hadisin yana bayyana cewa shigarsu aljanna ba kawai saboda aiki ba ne, kai babu makawa daga rangwamen Allah da rahamarSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -, su sun shigeta ne da sabubban ayyukansu, sai dai abinda ya tabbatar hakan shi ne rahamarSa - tsarki ya tabbatar maSa -, da rangwaminSa da gafararSa.

Bawa kada ya ruɗu ya yi jiji da kai da aikinsa duk yadda ya kai; domin cewa haƙƙin Allah (shi ne) mafi girma daga aikinsa, to babu makawa ga bawa daga tsoro da kwaɗayi gaba ɗaya.

Falalar Allah da rahamarSa ga bayinSa (ita ce) mafi yalwatuwa daga ayyukansu.

Ayyuka na gari sababi ne na shiga aljanna, rabauta da ita kuwa kaɗai daga falalar Allah ne da kuma rahama daga gareShi.

AlKarmani ya ce: "Idan dukkanin mutane ba zasu shiga aljanna ba sai da rahamar Allah, to fuskantar keɓantar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ambato shi ne cewa shi idan ya kasance a yanke cewa shi zai shiga aljanna, kuma shima ba zai shigeta ba saida rahamar Allah; to waninsa zai zama a hakan ta hanyar ne mafi cancanta.

Al-Nawawi ya ce: A cikin ma'anar faɗinsa - Allah Maɗaukakin sarki -: {Ku shiga aljanna saboda abinda kuka kasance kuna aikatawa} [al-Nahl: 32],

{Wancan aljannar da aka gadar muku da ita saboda abinda kuka kasance kuna aikatwa} [al-Zukhruf: 72], da makamancinsu na ayoyin da suke nuni akan cewa ayyuka ana shiga aljanna da su, to ba ya karo da waɗannan hadisan, kai ma'anar ayoyin cewa shiga aljanna da sababin ayyuka ne, sannan gamkatar ga ayyuka, da shiriya dan tsarkakewa a cikinsu, da kuma karɓarsu da rahamar Allah - Maɗaukakin sarki - da falalarSa ne, sai ya tabbata cewa shi ba zai shiga ba saboda mujarradin ayyuka, shi ne abin nufi da hadisan, kuma yana tabbata cewa shi ya shiga da ayyuka; wato: da sababinsu, kuma daga rahama ne.

Ibnul Jauzi ya ce: Amsoshi huɗu suna tabbata daga hakan; na farko: Lallai cewa gamkatar ga aiki daga rahamar Allah ne, da ba dan rahamar Allah da ta gabata ba da imani bai tabbata ko ɗa'ar da tsira yake faruwa da ita ba.

Na biyu: Lallai cewa abubuwan anfanin bawa ga mai shi ne to aikinsa abin cancanta ne ga mai shi, a duk lokacin da aka yi masa ni'ima na sakayya to shi daga falalarSa ne. Na uku: Ya zo a cikin wasu daga cikin hadisai cewa shi shiga aljanna da rahamar Allah ne, kuma rabe-raben darajoji da ayyuka ne.

Na huɗu: Lallai cewa ayyukan ɗa'a (biyayya) sun kasance a cikin ƙanƙanin zamani, kuma sakamako ba ya ƙarewa to ni'imtarwa wacce ba ta karewa a cikin sakamakon abinda yake karewa da falala bada fuskar ayyuka ba.

AlRafi'i ya ce: Lallai mai aiki kada ya dogara akan aikinsa a cikin neman tsira da samun darajoji; domin shi kawai ya yi aikin ne da dacewar Allah, kawai ya bar saɓo ne saboda tsarin Allah to dukkanin wannan da fallarSa ne da kuma rahamarSa.

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi