Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a

Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a".

[Hasan ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa babu wani abu a ibadu mafifici a wurin Allah sama da addu'a; domin a cikinta akwai iƙirari da wadatar Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -, da kuma iƙirari da gajiyawar bawa da buƙatuwarsa gareshi.

فوائد الحديث

Falalar addu'a kuma wanda ya roƙi Allah, to, shi mai girmamashi ne, kuma mai tabbatarwa ne da cewa Shi (Allah) Mawadaci ne - tsarki ya tabbatar masa - ba a roƙon mabuƙaci, kuma cewa Shi Mai yawan ji ne kurma ba a roƙonsa, kuma cewa shi mai kyauta ne, marowaci ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Mai jin ƙai ne mai bushewar zuciya ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Mai iko ne gajiyayye ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Makusanci ne manisanci ba ya ji, da wanin haka na siffofin ɗaukaka da kyau na Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.

التصنيفات

Falalar Addu'a