An kewaye wuta da sha'awowi, kuma an kewaye Aljanna da abubuwa ki

An kewaye wuta da sha'awowi, kuma an kewaye Aljanna da abubuwa ki

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "An kewaye wuta da sha'awowi, kuma an kewaye Aljanna da abubuwa ki".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wuta abar kewayewace da al'amuran da rai take son sha'awrsu na aikata abubuwan da aka haramta, ko takaitawa a wajibai; Duk wanda ya bi son ransa a hakan to ya cancanci wuta, Kuma cewa Aljanna abar kewayewace da al'amuran da rai take kin su; kamar lazimta akan abubuwan da aka umarta da barin abubuwan da aka haramta, da hakuri akan hakan, idan ya kutsa kuma ya yaki ransa a hakan to ya cancanci shiga Aljanna.

فوائد الحديث

Daga sabubban afkawa a sha'awowi kawatawar Shaidan abin ki da mummuna, har rai ya gan shi mai kyau ne, sai ya karkata zuwa gare shi.

Umarni da nisantar sha'awowin da aka haramta; domin cewa su hanya ce zuwa wuta, da kuma hakuri akan abubuwan ki; domin cewa su hanya ce ta zuwa Aljanna.

Falalar yakar rai ko kokari a ibada, da kuma hakuri akan abubuwan ki da wahalar da ke kewaye ayyukan biyayya.

التصنيفات

Sifar Al-janna da Wuta