Kada ku maida gidajanku kaburbura, kuma kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gareni; domin cewa salatinku a gareni yana isomin a duk inda kuke

Kada ku maida gidajanku kaburbura, kuma kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gareni; domin cewa salatinku a gareni yana isomin a duk inda kuke

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku maida gidajanku kaburbura, kuma kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gareni; domin cewa salatinku a gareni yana isomin a duk inda kuke".

[Ingantacce ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin hani daga wofintar da gidaje daga sallah sai su zama kamar makabartu, da ba'a sallah a cikin su. Kuma ya yi hani daga maimaita ziyarar wani kabari da taruwa a wurinsa ta fuskar al'ada; domin hakan hanya ce zuwa ga shirka, Ya yi umarni da yin salati da sallama a gare shi a kowane wuri anan doron kasa; domin cewa hakan yana isa gare shi daga na kusa da na nesa duk daya ne, babu bukatuwa zuwa kaikawo a kabarinsa.

فوائد الحديث

Hani daga wofintar da gidaje daga bautar Allah - Madaukakin sarki -a cikinsu.

Hani daga tafiya dan ziyarar kabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; domin cewa shi ya yi umarni da yin salati a gare shi kuma ya sanar da cewa shi yana isowa zuwa gare shi, kadai ana daure sirdi ne dan nufin masallaci da kuma sallah a cikinsa.

Haramcin sanya ziyarar kabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idi, ta hanyar maimaita ziyararsa ta kebantacciyar fuska a wani zamani kebantacce, hakanan ziyar kowanne kabari.

Girman Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa, ta hanyar shara'anta yin salati da sallama a gare shi a kowanne zamani da kuma kowanne wuri.

Yayin da cewa hanin game da sallah a wurin kaburbura hakika ya tabbata a wurin sahabbai; saboda haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana maida gidaje tamkar makabartun da ba'a sallah a cikin su.

التصنيفات

Falalar Ayyuka na qwarai