Annamimi ba zai shiga aljanna ba

Annamimi ba zai shiga aljanna ba

Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa; "Annamimi ba zai shiga aljanna ba".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

(Annabi) Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana ba da labarin cewa annamimi wanda yake cirato zance a tsakanin mutane da nufin ɓata tsakaninsu shi mai cancanta ne ga uƙubar cewa ba zai shiga aljanna ba.

فوائد الحديث

Annamimanci yana daga manyan zunubai.

Hani daga annamimanci; saboda abin da ke cikinsa na ɓatawa da cutarwa a tsakaknin ɗaiɗaiku da jama'u.

التصنيفات

Munanan Halaye