Idan dayanku zai yi alwala to ya sanya ruwa a hancinsa sannan ya face, wanda zai yi tsarkin hoge to ya yi shi wutiri

Idan dayanku zai yi alwala to ya sanya ruwa a hancinsa sannan ya face, wanda zai yi tsarkin hoge to ya yi shi wutiri

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Idan dayanku zai yi alwala to ya sanya ruwa a hancinsa sannan ya face, wanda zai yi tsarkin hoge to ya yi shi wutiri, idan dayanku ya farka daga baccinsa to ya wanke hannunsa kafin ya shigar da su a ruwan alwalarsa, domin cewa dayanku ba ya sanin a'ina hannunsa ya kasance". Lafazin Muslim: "Idan dayanku ya farka daga baccinsa kada ya nutsa hannunsa a cikin kwarya har sai ya wankesu sau uku, domin cewa shi ba ya sanin a'ina hannunsa ya sakance ".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana sashin huklunce-hukuncen tsarki, daga cikinsu: Na farko: Cewa wanda zai yi alwala to ya wajaba akansa ya shigar da ruwa a cikin hancinsa da numfashi, sannan ya fitar da shi ta numfashi kuma. Na biyu: Cewa wanda ya yi nufin tsarkake kazanta mai fita daga gareshi da gusar da ita ba tare da ruwa ba kamar duwatsu da makancinsu to tsarkakewarsa ta zama akan adadin mara mafi karancinsa uku, mafi yawa wanda zai kawar da abinda ya fita zai kuma tsarkake wurin. Na uku: Cewa wanda ya farka daga baccin dare kada ya shigar da tafinsa a cikin kwarya dan ya yi alwala har sai ya wankesu sau uku a wajen kwaryar, domin cewa shi bai san a'ina hannunsa ya kasance ba, ba zai iya amintar da najasa akan su ba, zai iya yiwuwa Shaidan ya yi wasa da su kuma ya dora abubuwa masu cutarwa garesu ga mutum ko mai bata ruwan.

فوائد الحديث

Shaka ruwa yana wajaba a cikin alwala, shi ne: Shigar da ruwa a cikin hanci ta hanyar numfashi, hakan nan facewa yana wajaba, shi ne: Fitar da ruwa daga hanci ta hanyar numfashi.

Anso mara a tsarkin hoge.

Halaccin wanke hannaye bayan baccin dare sau uku.

التصنيفات

Ladaban biyan bukata, Ladaban biyan bukata, Alwala, Alwala, Ladaban bacci da kuma tashi daga Bacci, Ladaban bacci da kuma tashi daga Bacci