إعدادات العرض
Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin
Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin
Daga Khaulah ’Yar Hakim Al-Sulamiyyah, ta ce: Na ji Ma’aikin Allh tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin.
الترجمة
العربية Bosanski English Español فارسی Français اردو 中文 हिन्दी Bahasa Indonesia বাংলা Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் සිංහල မြန်မာ Русский ไทย Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە Türkçe دری Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy Română Kinyarwanda नेपाली Српски Wolof Soomaali Moore Українська Български Tagalog Azərbaycan ქართული тоҷикӣ bm Oromoo Македонскиالشرح
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana nunawa al’ummarsa mafaka da matsera masu amfani, waɗanda za su kawar masa da duk abin da mutum yake tsoro, a lokacin da yake a wani wuri a nan doran ƙasa, shin yana halin tafiya ne ko shaƙatawa, ko wanin haka: sai ya nemi tsari da mafaka da kalmomin Allah cikakku a falalarsu da albarkarsu da amfaninsu, wanda ba su da kowane aibi da tawaya, daga sharrin duk abin halitta, to, sai ya amintu a inda ya sauka, muddin yana nan babu abin da zai cutar da shi.فوائد الحديث
Neman tsari ibada ne, kuma shi ne abin da ya kasance daga Allah maɗaukaki ko sunayanSa ko kuma siffofinSa.
Halaccin neman tsarin Allah da zancenSa, domin sifa ce daga cikin siffofinSa mai tsarki, saɓanin neman tsari daga wani abin halitta wannan shirka ne.
Falalar wannan Addu’ar da kuma albarkarta.
Neman mafaka da zikiri dalili ne na tsare bawa daga sharri.
Lalata neman tsari da wanin Allah kamar aljan da matsafa da shedanu da sauransu.
Shar’antuwar wannan Addu’ar ga duk wanda ya sauka wani wuri a halin zaman gida ko tafiya.