Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare

Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare

Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare, idan zai shiga bai ambaci sunan Allah a yayin shigarsa ba, Shaidan zai ce: Kun sami makwanci, idan bai ambaci Allah a lokacin cin abincin sa ba, zai ce : Kun riski makwanci da abincin dare".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da ambatan Allah a yayin shiga gida da kafin cin abinci, kuma cewa shi idan ya ambaci Allah da fadinsa: (Da sunan Allah) a lokacin shigarsa da kuma lokacin fara abincinsa, Shaidan zai cewa mataimakansa: Baku da rabo na makwanci ko abincin dare a wannan gidan da mai shi ya kare kansa daga ku da ambatan Allah - Madaukakin sarki -. Amma idan zai shiga gidansa bai ambaci Allah a lokacin shigarsa ba ko lokacin cin abincinsa, sai Shaidan ya sanar da mataimaknsa cewa sun sami makwanci, da abincin dare a wannan gidan.

فوائد الحديث

An so ambatan Allah a lokacin shiga gida da lokacin cin abinci, domin Shaidan yana kwana a cikin gidaje, yana ci daga abincin mutanen gidan idan ba su ambaci sunan Allah - Madaukakin sarki ba -.

Shaidan yana lura da Dan Adam a cikin aikinsa da jujjuyawarsa acikin al'amauransa gaba dayansu, idan ya rafkana daga zikiri zai samu abin nufinsa daga gare shi .

Zikiri yana kore Shaidan.

Kowanne Shaidan yana da mabiya da masoya suna albishir da maganarsa kuma suna bin umarninsa.

التصنيفات

Koyarwar Manzon Allah SAW a cikin Zikiri, Fa’idojin Ambaton Allah Maigirma da xaukaka, Zikiri da ba su da wani Qaidi