Kowa ne aikin alheri sadaka ne

Kowa ne aikin alheri sadaka ne

Daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kowa ne aikin alheri sadaka ne".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa dukkanin kyautatawa da amfani ga wasu na magana ne, ko na aiki yana zama sadaka, kuma a cikinsa akwai lada da sakamako.

فوائد الحديث

Lallai sadaka ba ta taƙaituwa a abin da mutum yake fitar da shi daga dukiyarsa, kai, yana tattaro kowane alherin da mutum zai aikatashi, ko ya faɗeshi ya sadar da shi zuwa wasu.

A cikinsa akwai kwaɗaitarwa a kan yin aikin alheri da dukkanin abin da a cikinsa akwai amfani ga wasu.

Rashin wulaƙanta wani abu daga aikin alheri ko da ya zama ƙarami ne.

التصنيفات

Falalar Ayyuka na qwarai, Falalar Ayyuka na qwarai